Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anyi Gargadi Kan Saida Maganin Zazzabin Cizon Sauro Mara Kyau a Kasar Ghana


Kwayoyin magunguna
Kwayoyin magunguna

Hukumar abinci da magunguna ta kasar Ghana tana gargadin jama’a, musamman asibitoci, wuraren shanmagani, wurin saida magani da sauran wuraren kiwon lafiya, game da kasancewar wani maganin zazzabin cizon sauro mara kyau a kasuwannin kasar Ghana, mai suna – kwayoyin Quinine Sulphate (300mg).

Hukumar abinci da magunguna ta kasar Ghana tana gargadin jama’a, musamman asibitoci, wuraren shanmagani, wurin saida magani da sauran wuraren kiwon lafiya, game da kasancewar wani maganin zazzabin cizon sauro mara kyau a kasuwannin kasar Ghana, mai suna – kwayoyin Quinine Sulphate (300mg).

A fadar wannan hukumar, wannan maganin har yanzu ba’a tabbatar da ingancin shi ba. Haka kuma hukumar ta yi nuni da cewa St Kem Pharmaceuticals Limited, wadanda ke da ofishin su a Patasi, Kumasi (gefen ofishin ‘yan sanda) da Achimota, Accra, ( hawa na farko na Dokua Plaza) sune suke shigo da maganin suna kuma rarrabashi a cikin kasar Ghana.

Maganin ya kunshi abubuwa kamar su:

Lambar Jikinsa: 33587Q, Ranar da akayi shi: Mayu, 2012, Ranar da zai dena aiki: Mayu, 2015, Kamfanin da sukayi shi: Biochemie GmbH, Vienna, Austria

Hukumar ta FDA ta ce, wannan maganin yana cikin kwali fari na roba, wanda ke dauke da kwayoyi 1000, da wannan rubutu 'SHIRIN SAMAR DA MUHIMMAN MAGUNGUNA’ da kuma dauke da bayanan da aka rubuta na sama.

Hukumar FDA tace a yayin wani bincike da ta gudanas a kasuwannin magunguna, ta kwace kimanin katan 64 mai dauke da yawan kwayoyi 1000 kowanne (wato kwayoyi 64,000) a Asibitin Dormaa Presbyterian a sashin Brong Ahafo da kuma St Kem Pharmaceuticals Limited a Kumasi.

Domin haka tana gargadar asibitoci, mashayar magani, wuraren sayar da magunguna da iri- irinsu dake dauke da wannan maganin zazzabin cizon sauron na Quinine marasa kyau da suyi sauri su mika su ga wannan hukumar mafi kusa dasu.

Hukumar FDA tayi gargadin jama’a da cewa, "kada su sayi wannan maganin kuma su kai rahoton dukan wanda suka samu yana sayas da wannan maganin ga FDA.
Wannan bayanin ya kara da cewa, jami’an tsaro sun gayyaci masu samas da wannan magnin domin su taimaka wajen binciken da ake kan gudanaswa

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG