Kasar Equatorial Guinea ta sanar da bullar kwayar cutar Marburg ta farko, cuta mai saurin yaduwa kamar Ebola, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Ministan tsaron kasar Ghana ya ce wasu ‘yan tada zaune tsaye sun yi kokarin tarwatsa wata gada da bama-bamai a karon farko a garin Bawku da ke kasar, lamarin da kwararru ke cewa zai iya ingizo kan masu tsattsauran ra’ayin addini daga kasar Burkina Faso da ke iyaka da Ghana.
Akalla ma’aikatan noman ayaba biyar ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a ranar Juma’a a yankin Kudu maso yammacin Kamaru da ke fama da rikicin ‘yan aware, in ji wani shugaban kungiya.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun tabbatar da mutuwar dakarun kasar 10 tare da bacewar wasu sama da 10 sakamakon kwanton baunar da ‘yan ta’adda suka yi wa ayarin motocin soja a ranar juma’a lokacin da suke sintiri a wani kauyen jihar Tilabery iyaka da kasar Mali.
Hukumar kiwon lafiyar al’ummar Jamhuriyar Nijar ta ayyana samun nasarar kawar da cutar makantar kuda wato Onchocercose ko River Blindness daga kasar bayan fafutukar shekaru sama da 40.
Kungiyoyin fafutika sun bukaci hukumomin kasar Nijar su saki shugaban gamayyar M62 Abdoulaye Saidou, bayan tsare shi da aka yi na tsawon mako 2 bisa zarginsa da tada gobara da gangan a mahakar zinaren Tamou, sai dai masu rajin kare dimokaradiya na cewa a daina yi wa sha’anin shari’a katsalandan.
Najeriya da Nijar na ci gaba da karfafa matakan da za su bada damar gaggauta kammala shirinsu na shimfida layin dogo a aikace daga Jihar Kano a Najeriya zuwa Maradi da zai ratsa ta wasu garuruwan Jihar Katsina a Najeriya.
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun cafke wasu tsofaffin shugabannin hukumar shigi da ficin kaya a ci gaba da binciken da hukumar yaki da cin hanci ta kaddamar kan wata badakalar da ta shafi dubban miliyon cfa wace ake hasashen za ta iya rutsawa da dimbin jami’an Douane, wato kwastam.
Kotun shari’ar rigingimun kasuwanci ta umurci hukumar Alhazai ta Nijar da ta mayar wa wasu maniyyata daruruwan miliyoyin cfa na kudaden da su ka biya amma kuma aka kasa kai su aikin Hajji.
Wani binciken kwararru a kasar Faransa ya gano cewa kanfanin Cominak dake hako karfen uranium a Arlit dake Jamhuriyar Nijar, ya zubar da tan milyan 20 na sinadari mai tururin guba (radioactivite) bayan ya shafe sama da shekaru hamsin yana gudanar da aikinsa a yankin.
Domin Kari