Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya amince da Ghana rancen dala biliyan 3, kasar da ke fuskantar matsin tattalin arziki. Kason farko na dala miliyan 600 zai shiga asusun Bankin Ghana ranar Juma’a 19 ga Mayu, a cewar gwamnan Bankin Ghana, Ernest Addison.