Wani kwale-kwale ya nutse a tekun Sfax mai tashar jiragen ruwa na kasar Tunisiya, inda mutane biyar suka mutu, wasu bakwai kuma suka bace, in ji jami'ai a jiya Talata.
Masu rajin kare hakkin bil’adama a Nijar sun ce sun kasa samun damar ganawa da manyan jami’an siyasa da aka tsare bayan da sojojin juyin mulki suka hambarar da zababben shugaban kasar ta Afirka kusan makonni uku da suka gabata.
Shugaban sojojin Mali Assimi Goita ya fada a ranar Talata cewa ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin game da halin da ake ciki a Nijar, inda sojoji suka kwace mulki a wani juyin mulki a watan jiya.
Kiristoci daga Najeriya, Nijar da Chadi sun shafe kwanaki bakwai suna gudanar da addu'o'i ga kasar ta Nijar dama Nahiyar Afrika baki daya.
Wannan sabuwar dambarwa ta kunno kai ne kwana guda bayan da wata tawagar manyan malaman addinin Islama daga Najeriya ta kai ziyarar shiga tsakani a rikicin siyasar kasar.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun ce za su tuhumi hambararren Shugaban kasar Mohamed Bazoum da laifin “cin amanar kasa” da kuma yi wa sha’anin tsaron kasa zagon kasa.
Tawagar manyan malaman Islama na Najeriya da ta gana da shugaban gwamnatin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ta ayyana nasarar ziyarar.
Wata tawagar malaman addinin Islama ta ziyara a birnin Yamai a ranar Assabar inda suka gana da shugabannin mulkin sojin jamhuriyar Nijar da suka hada da Janar Abdourahamane Tchiani da Firai Minista Ali Mahaman Lamine Zeine.
Wasu 'yan Nijar na ganin Faransa ba ta tabuka wani abin a-zo-a-gani a yakin da take yi da ayyukan ta'addanci a kasar da ma yankin Sahel baki daya.
Rundunar sojan Nijar ta shaida wa wani babban jami’in diflomasiyyar Amurka cewa, za su kashe Bazoum idan kasashen da ke makwabtaka da kasar suka yi yunkurin shiga tsakani na soji don maido da mulkinsa, kamar yadda wasu jami’an kasashen yammacin duniya suka shaida wa kamfanin dillancin labaran AP.
Domin Kari