Matsalar karancin takardun kudi na CFA na ci gaba da ta’azzara a sassan Nijar sakamakon takunkuman kasashen Africa ta Yamma Rainon Kasar Faransa, cewa da UEMOA da suka sanya wa kasar Nijar bayan juyin mulki inda suka hana shiga da takardun kudin CFA a bankunan kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da mutuwar wani mutum da ake zargi da kisan kishi wanda ya ke gudun gurfana gaban kotun bin kadin manyan laifuka ta duniya.
Kashi 40 cikin 100 na Manoma a jihar Agadas da ke arewacin Jamhuriya Nijar sun kaurace wa gonakinsu, inda suka koma harkar neman zinari bayan da suka samu kansu a halin tsaka mai wuya sakamakon matsalar karancin ruwan sama da aka samu a bana.
Kungiyar ‘yan jarida ta Ghana (GJA) tare da hadin gwiwar ofishin jakadancin Amurka a kasar sun kaddamar da wani shiri na tabbatar da kwarewa a ayyukan kafafen yada labarai don babban zaben shekarar 2024 da ke tafe, da nufin kare dimokradiyyar kasar.
Shekaru 8 bayan kafa dokar hana safarar bakin haure dake kwarara a Jamhuriyar Nijar da nufin tsallakawa zuwa nahiyar Turai a ‘yan kwankinnan, matsalar ta dawo gadan-gadan inda a tashoshin mota ake samun karuwar bakin haure daga Yammancin Afirka dake son gwada sa’ar su.
Kinshasa tana zargin Kigali da taimakawa ayyukan kungiyar ‘yan tawaye M23 a gabashin DR Congo, yayin da ita Rwandan ke zargin Congo da taimakawa ayyukan kungiyar ‘yan tawayenta ta Democratic Forces for Liberations of Rwanda FDLR.
Kungiyar matasan lauyoyi ( AJAN) a Jamhuriyar Nijar ta nuna damuwa game da yawaitar kame -kamen mutane tare da tsare su ba a kan ka’ida ba duk da cewa sojojin da suka yi juyin mulki a watan Yulin 2023 sun sha alwashin mutunta yarjeniyoyin kasa da kasar da Nijar ta saka hannu.
Rundunar mayakan Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa an fara cin karfin ayyukan kwashe dakarun Faransa daga kasar ta Nijar.
A jamhuriyar Nijar yau wasu ‘yan kasar, da hadin gwiwar al’ummomin kasashen yammacin Afrika mazauna kasar, su ka yi zaman darshan a harabar kungiyar CEDEAO ta birnin Yamai da jan hankulan shugabannin kasashen yankin kan bukatar su janye takunkumin da suka kakaba bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan wasu mutane a lokacin da suke barci a wani gari da ke yammacin kasar Kamaru kamar yadda wani jami'in karamar hukumar ya sanar a safiyar ranar Litinin, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum akalla 20.
Kungiyoyin farar hula sun yi gangami ranar Lahadi a birnin Yamai da nufin nuna bukatar mahukunta su kadammar da farautar mukarraban gwamnatin PNDS Tarayya, cikinsu har da shugaba Issouhou Mahamadou da suke zargi da handamar dukiyar kasa, sai dai magoya bayan tsohon shugaban sun yi watsi da batun.
Yayin da kungiyoyin farar hula ke ci gaba da maida martani kan matakin amincewa da juyin mulkin sojoji a Nijar da kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta yi, hukumomin mulkin sojojin Nijar sun bukaci tattaunawa da ECOWAS domin warware rikicin siyasar kasar cikin ruwan sanyi.
Domin Kari