Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Tabbatar Da Mutuwar wani Dan Ruwanda Da Ake Zargi Da Kisan Kiyashi


Muhammadu Buhari a lokacin da yake jawabi a Majalisar Dinkin Duniya
Muhammadu Buhari a lokacin da yake jawabi a Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da mutuwar wani mutum da ake zargi da kisan kishi wanda ya ke gudun gurfana gaban kotun bin kadin manyan laifuka ta duniya.

Mai gabatar da kara, wanda aikinsa ne neman sauran masu laifin da ke boye wa kotun duniya da ke shari’ar manyan laifukan da aka tabka a Rwanda, yau Talata ya tabbatar da mutuwar Aloys Ndimbati, wanda ake zargi da aikata kisan kiyashi.

Cikin shekaru uku da su ka gabata, kotun ta kasa da kasa mai shari’ar manyan laifuka ta IRMCT, ta kama wasu ‘yan Rwanda biyu da ake zargi da taka rawa a kisan kiyashi, sannan ta kuma tabbatar da mutuwar wasu masu guje ma kotun su hudu, ciki har da Ndimbati.

A wani bayani, masu gabatar da kara na MDD, sun gamsu cewa Ndimbati ya mutu a Rwanda tun a 1997.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG