A jawabin shi sabon jami'in yada labarai na kungiyar dattawan ta arewa da farfesa Ango Abdullahi ke jagoran ta, Malam Abdul'aziz Sulaiman, ya ce ya zama wajibi 'yan arewa su hada kai wajen kawar da bambance-bambance da fuskantar abubuwan da za su dawo da zaman tare a yankin.
Al’ummomin kasashen Jamhoriyar Nijar da Najeriya na ci gaba da yin kiraye kirayen ganin an bude bodar kasar Nijar tare da janye takunkumin da aka kakaba wa kasar ta Nijar bayan juyin mulkin da sojoji su ka yi a ranar 26 ga watan Yuli.
Mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a Kenya ta yi sanadiyyar rasa rayuka da dama, ta kuma lakume rayukan dabbobi da rushe daruruwan gidajen jama'a.
Yan gudun hijirar Najeriyar da ke Chadi sun gujewa sansanin da ake tsugunar da su saboda cunkoso inda da dama daga cikinsu suka nemi mafaka a gidan Sarkin Hausawan Adre da ke Chadi.
Sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar sun soke dokar da ta taimaka wurin rage kwararar ‘yan kasashen Yammacin Afirka zuwa Turai musamman mazauna karkara wadanda ke fama da matsin tattalin arziki da suka dade suna dogara da ci-rani.
Rashin aikin yi ya yi kamari a wurare kamar tsohon birnin Agadez wanda ya zama babbar mashigar yankin Sahara da masu safarar ke ratsawa da bakin haure.
Ana samun makamashin hasken rana sosai a Nijar, yankin da ke kudu da Sahar hamada a yammacin Afrika. Akwai farantan tatsar hasken rana fiye da 55,000 da aka sanya a cibiyar.
A ranar Lahadi ne mahara suka yi musayar wuta da jami'an tsaro a babban birnin Saliyo tare da kai hari kan babban barikin sojan kasar da manyan gidajen yari, ciki har da gidan yarin da ke da dubban fursunoni.
Shirin da kasar take fata zai taimaka wajen bunkasa harkokin yawon bude ido da kuma tattalin arzikin kasar.
Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio, ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar a yau Lahadi bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a babban barikin sojoji kuma mafi girma a babban birnin kasar Afirka ta Yamma, sannan suka mamaye wuraren da ake tsare da mutane ciki har da wani babban gidan yari.
Kungiyar mai suna EAC a takaice, na dauke da kasashen Burundi, Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, Kenya, Rwanda, Sudan ta Kudu, Tanzania da kuma Uganda.
Shugaban Faransa ya ce a shirye yake ya tattauna da jagororin juyin mulkin Nijar amma bisa sharadin sakin hambararren shugaba Bazoum Mohamed. Macron ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da shugaban Ivory Coast Alasane Ouattara, lamarin da masana ke ganin kasar Faransa ta sassauto daga matsayarta.
Domin Kari