Da ya ke yanke hukunci a ranar Alhamis, mai shari'a Dupe Atoki ya kira gwamnatin sojin Nijar da haramtacciya, wadda ta saba wa kundin tsarin mulkin Nijar, saboda haka ba'a amince da ita a matsayin mamba a kungiyar kasashen yankin ba.
Al'ummar Jamhuriyar Nijar sun fara maida martani bayan da kotun ECOWAS a zamanta a yau Alhamis ta kori karar da hukumomin mulkin sojan kasar suka shigar da nufin kalubalantar jerin takunkumin da kungiyar ta kakaba wa Nijar sanadiyar juyin mulkin 26 ga watan Yuli.
Jamhuriyar Nijar da kasar Mali sun bada sanarwar yanke huldar sassaucin harajin da suka kulla da Faransa a karkashin wasu yarjeniyoyin da aka rattaba wa hannu yau shekaru sama da 50 din da suka gabata.
Matsalar sace sace na cigaba da tayar da hankulan jama’a a arewacin Nijar. Ana dai danganta yawaitar sace sacen da tururuwar da baki 'yan Africa ta Yamma ke yi a cikin jihar Agadas bayan da gwamnatin mulkin soja ta soke dokar hana safarar bakin haure kwanaki biyar da su ka gabata.
Wata babbar kotu a Accra ta daure wata yar kasar China mai suna Aisha Huang wadda tayi fice wajen hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba shekaru hudu da rabi a gidan kaso bayan da aka same ta da wasu laifuka ciki harda hakar ma'adinai ba bisa kaida ba, da shiga kasar ta barauniyar hanya.
Sabuwar jakadiyar Amurka ta gabatar wa hukumomin rikon kwaryar Nijar takardun kama aiki, kwana daya bayan haka Rasha ta tura karamin ministanta na tsaro zuwa birnin Yamai, ziyarar da masana suka fassara a matsayin wani yunkuri na Rasha na samun matsuguni a Yankin Sahel.
Watanni sama da hudu bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar jama'a na ci gaba da fuskantar tsadar rayuwa sakamakon karayar tattalin arziki tun bayan takunkumin da kungiyoyi irinsu ECOWAS ko CEDEAO suka lafta wa Nijar.
Ministan harkokin wajen Najeriya ya ce har yanzu kungiyar ECOWAS na a shirye ta tattauna da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar kuma sai in sojojin sun saki Bazoum ne za a fara tattaunawar cire takunkumin da aka sanya wa Nijar.
An kara yawan ‘yan sanda masu sintiri a daya daga cikin garuruwan da aka fi samun tashe-tashen hankula a Afirka ta Kudu a ranar Lahadi, bayan da wani gungun jama’a suka daure kana suka kona wasu mutane bakwai da ake zargi da aikata laifuka, a cewar ‘yan sanda da mazauna yankin.
Jamhuriyar Nijar ta bi sahun sauran takwarorin ta na duniya wajan tunawa da ranar yaki da cutar Sida.
Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana matukar damuwa da matakin da sojojin da ke mulki a Nijar suka dauka na soke dokar da ta haramta safarar bakin haure daga cikin kasar zuwa Turai ta hanyar ratsa sahara dake da matukar hadari
Matasan sun nuna bacin ran su ne game da zargin wani dan sanda da suka ce ya harbe wani dan Uwan su a Unguwar Kurna, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar shi bayan an garzaya da shi Asibiti.
Domin Kari