Kwanaki 3 bayan da kungiyar ECOWAS ta sanar da janye wani bangare na takunkumin da ta kakaba wa Nijar, an fara samun sauyi a harkokin yau da kullum a kasar inda a cikin daren Laraba, Najeriya ta mayar da wutar lantarkin da ta saba bayarwa yankunan da yarjejeniyar kasashen biyu ta shafa.
Majalisar dokokin Ghana ta amince da kudurin dokar hana auren jinsi mai cike da cece-kuce bayan an shafe kusan shekaru uku ana tattaunawa.
Hukumar sadarwa ta kasar Ghana NCA, ta sanar da rufe gidajen rediyo saboda gudunmuwar da suke bayarwa wajen ruruta wutar rikicin kabilanci da yaki ci yaki cinyewa a yankin Bawku na jahar maso gabashin kasar Ghana.
Masu aikin ceto sun zakulo gawarwaki fiye da 20 daga tekun arewacin Senegal a ranar Laraba bayan da wani kwale-kwalen da ke dauke da bakin haure da ke kan hanyar zuwa Turai ya nutse, kamar yadda wani gwamnan yankin ya shaida wa AFP.
An yi ta harbe-harbe a babban birnin kasar Chadi a kusa da hedkwatar jam'iyyar adawa, bayan wata arangama da aka yi cikin dare a kusa da hukumar tsaron cikin gida ta kasar wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Hukumar zaben kasar Chadi ta ba da sanarwar ba zato a ranar Talata cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasa wanda zai kawo karshen mulkin soji na tsawon shekaru uku a yankin tsakiyar Afirka a ranar 6 ga watan Mayu.
Gwamnatin mulkin soja ta Guinea ta fada jiya talata cewa ta nada sabon firaminista kwanaki takwas bayan rusa gwamnatin da ta shude, yayin da harkoki a Conakry, babban birnin kasar su ka tsaya cik a rana ta biyu ta yajin aikin gama gari.
Ana yawan samun hadurran ababen hawa a kasar Mali, inda manyan tituna da kuma ababen hawa ba su da kyau.
Kasar Burkina Faso na daga cikin yankin kudu da hamadar sahara da ke fama da tashe tashen hankula tun bayan yakin basasar Libya a shekara ta 2011.
Najeriya ta amince da dawo da hasken wutar lantarki ga jamhuriyar Nijar bayan janye wasu takunkumai da Kungiyar Raya Tattalin Arziki Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, ta yi kan kasar.
Matakin dage wa kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso da kuma Guinea takunkumin da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta sanar a karshen taron shugabannin kasashen Yammacin Afirka da ya gudana a wannan Asabar 24 ga watan Fabrairu a Abuja ya saka farin ciki a zuciyoyin jama’ar jamhuriyar Nijar.
Domin Kari