Afrika ta Kudu zata gudanar da babban zabenta a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa, zaben da ake sa ran ya zama mafi fafatawa a yakin neman kuri'u tun bayan fara mulkin dimokradiya a kasar a shekarar 1994.
A yayin da Kiristoci a fadin duniya baki daya ke fara shirnin gudanar da bukukuwan Istan wannan shekar, fastoci na bayyana muhimmancin Good Friday kamar yadda Bishara mai tsarki ta nuna.
Ma'aikatar sufuri a Afirka ta Kudu ta sanar cewa wata motar bas ta fado daga wata gada kuma ta kama wuta ranar Alhamis, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 45 daga cikin 46 da ke cikin bas din.
Sama da mako guda bayan da hukumomin jamhuriyar Nijar suka bada sanarwar yanke huldar ayyukan soja da Amurka gwamnatin Amurkar ta ce ta yi na’am da wannan mataki saboda haka nan gaba kadan kasashen biyu zasu tattauna kan hanyoyi mafi amfani wajen kwashe sojojin Amurkan daga kasar.
Nasarar zaben shugaban kasar ta ranar Lahadi ta kasance wani gagarumar ci gaba ga Faye, wanda aka saki daga gidan yari kasa da makwanni biyu da suka wuce, kuma yanzu ya zama shugaban mafi karancin shekaru a kasar ta yammacin Afirka.
A ranar Talata ne gwamnatin Kenya ta fara mika gawarwakin 'yan kungiyar asiri 429 ga 'yan kungiyar asiri da ake musu shari'ar da ta girgiza kasar.
Akalla sojoji bakwai ne suka rasa rayyukansu yayin da wani bam ya tashi a Chadi a yayin da suke sintiri a yammacin kasar kusa da tafkin Chadi, in ji gwamnatin kasar.
Dan takarar gamayyar jam'iyyu masu mulki, Amadou Ba, ya taya abokin hamayyarsa, kuma jagoran 'yan adawa a Senegal Bassirou Faye, murnar lashe zaben shugaban kasar Senegal.
Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashen yammacin Afirka da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda da ya bazu daga kasar Mali cikin shekaru 12 da suka gabata, lamarin da ya lakume rayukan dubban mutane tare da raba miliyoyin jama'a da muhallan su.
Ana gudanar da zaben ne makonni bayan da shugaba Macky Sall ya yi kokarin jan lokacin zaben har zuwa karshen shekara, hakar da ta ka sa cimma ruwa.
Wata babban jami’ar ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta shaidawa Majalisar a ranar Alhamis cewa, Amurka ba ta samu wata bukata a hukumance daga gwamnatin Nijar na ficewa daga kasar ba.
Wani harin kwanton bauna da aka kai a yammacin Laraba a yankin Tilabery kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar da kasashen Mali da Burkina Faso ya yi sanadin rasuwar dakarun kasar sama da 20 wasu 17 suka jikkata.
Domin Kari