Kungiyoyin bunkasa harshen Hausa da al’adun Bahaushe a Jamhuriyar Nijar sun gudanar da bikin tunawa da ranar Hausa ta duniya kamar yadda bikin ke gudana a kasashen Hausa a wannan Litinin 26 ga watan Agusta.
Ministan sadarwa Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo, ya kwatanta harin a matsayin “ragwanci” da wani “gungun masu laifi” ya kai.
Akalla mutum 21 da suka hada da kananan yara 11 ne suka mutu sakamakon wani harin da jiragen yaki mara matuka a ranar Lahadin da ta gabata a garin Tinzaouaten da ke arewacin kasar Mali, kusa da inda sojojin kasar suka yi mummunan rauni a watan da ya gabata, in ji 'yan tawayen Abzinawa
‘Yan jaridar kasashen Afrika masu amfani da harshen Hausa sun gudanar da taro a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijer inda suka tattauna kan gudunmawar ‘yan jaridar Hausa wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasashe.
Shugaban Tunisiya Kais Saied ya maye gurbin ministoci daban-daban da suka hada da na harkokin waje da na tsaro, fadar shugaban kasar Tunisiya ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin Facebook ba tare da wani bayani ba ranar Lahadi.
Taron a cewar wata sanarwa da hukumomin Saudiyya suka fitar a ranar Juma’a, za a yi shi ne tare da hadin gwiwar Kungiyar Hadin kan kasashen Musulmi ta OIC a ranar 26 ga watan Oktoban 2024.
Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun dauki matakin sassauta yawan kudaden da marasa lafiya ke biya a asibitocin gwamnati da kashi 50% yayin da kuma za a fara karbar haihuwa da wankin koda kyauta a ci gaba da bullo da matakan inganta rayuwar talakawan kasar.
Adadin wadanda suka mutu sakamakon hatsarin kwale-kwalen a yammacin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ya karu zuwa akalla 29 tare da gano akalla mutum 128 da suka tsira da rayukansu, wasu kuma ba a san adadinsu ba, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar a ranar Alhamis.
Hukumomin mulkin sojan Burkina Faso, Mali da Nijar sun rubutawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wasika domin yin Allah-wadai da zargin goyon bayan da kasar Ukraine ke yi wa kungiyoyin 'yan tawaye a yankin Sahel da ke yammacin Afirka, kamar yadda kwafin wasikarsu ta nuna.
A ci gaba da nasara da ake yi kan mayakan Boko Haram a kasashen Najeriya, Chadi, Kamaru, da Nijar, an sake samun wasu daga cikin 'yan bindigar da su ka mika wuya a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar
Domin Kari