Hukumomin lafiya a kasar Sudan sun sanar a ranar Lahadi cewa cutar barkewar cutar amai da gudawa ta yi sanadin mutuwar mutane kusan dozin biyu tare da jikkata wasu da dama.
Farin da ya faro tun a farkon shekarar nan ta 2024, kuma ya shafi amfanin gona da kiwo, lamarin da ya janyo karancin abinci da kuma illa ga tattalin arzikin kasashe da dama.
Wasu ‘yan kasar ta Nijar ne a karkashin wani kwamiti mai zaman kansa suka shiga tsakani har aka cimma nasarar kubutar da wadanan sojoji da tuni suka gana da shugaban gwamnatin mulkin soja Janar Abdourahamane Tiani a yammacin a ranar Alhamis.
Jami’an gwamnatin Uganda sun ce adadin mutanen da su ka mutu sanadiyyar gocewar kasa a ranar Asabar, a wani babban juji da ke Kampala babban birnin kasar ya karu zuwa 26, baya ga mutane 36 da har yanzu ba a san inda su ke ba.
Tsohon shugaban kasar a wannan wasika mai shafuka biyu ya jaddada cewa yana Allah-wadai da juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023 a kasar.
Cibiyar Kula da ke yaki da cututtuka da kariya ta Afirka ta bayyana a wannan makon cewa karuwar yaduwar kyandar biri a fadin nahiyar wani lamari ne da ke bukatar matakan gaggawa.
'Yan tawayen kasar Kamaru sun sake shiga gallaza ma mutanen kasar a cewa hukumomi. Tuni dai mutane su ka shiga gudu daga wuraren da 'yan tawayen ke tsananta ma mutane
Har yanzu ba a tantance yawan gawarwakin mutanen da ke karkashin tarkacen shara a birnin Kampala na Uganda ba.
Ma’aikatar cikin gida ta Jamhuriyar Nijar ta hana wani rangadin da hukumar UNDP ta kudiri aniyar gudanarwa a jihohin kasar da nufin bitar yanayin tsaron da ake ciki, wanda ba a bayyana dalilan daukan wannan mataki ba.
Adadin wadanda suka mutu sakamakon ruftarwar wani tudun bola a babban birnin Uganda ya karu zuwa 24 a ranar Litinin din nan yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da neman wadanda abin ya shafa a cewar hukumar birnin.
Rikicin ya samo asali ne daga yunkurin kashe al-Baqra da aka yi a ranar Juma’a, wanda mayakansa suka daura alhakinsa kan al-Shahida Sabriya, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito.
Mazauna iyakokin Nijar da Najeriya ne a kowane bangare, ke ci gaba da kokawa da matsalolin da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da aka yi a Najeriya ta haifar musu.
Domin Kari