Shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, a karon farko ya mayar da martani kan sukar da ake masa dangane da zargin hannu a kamawa da kuma daure wasu masu fafutukar yaki da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, da aka fi sani da ‘Galamsey’ a Ghana.