Majalisar dokokin Ghana ta amince da wani kudurin doka da za ta haramta zargin mutane da maita; Mutane da dama a sassan Najeriya su na sukar shirin gwamnatin kasar na raba tallafin rage radadin rayuwa, da wasu rahotanni
Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta ware sama da Naira miliyan 800 don gudanar da auren mutane 1,800 lokaci daya a karkashin wani shirinta na aurar da zaurawa; Wani matashi injiniya a Maiduguri ya na kera keke mai amfani da lantarki don baiwa mutane samun saukin zirga-zirga, da wasu rahotanni
Kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya RIFAN, ta ce sama da masana’antun shinkafa 50 a jihar Kano aka rufe saboda karancin shinkafa a fadin kasa; Wasu manoma mata da miji ‘yan asalin Najeriya mazauna Amurka suna amfani da fasaharsu wajen inganta sana’arsu ta noma a jihar Maryland, da wasu rahotanni
Shugaban Ghana Nana Akufo Addo, ya sanya hannu kan kudirin dokar da Majalisar Dattawan Ghana ta amince na soke hukuncin kisa; Shugabannin mata na Fulani sun ce mata za su iya taka muhimmiyar rawa wajen rage takun saka tsakanin manoma da makiyaya, da wasu rahotanni
Glacoma shike kan gaba wajen haifar da makantar da idanu basa a sake gani na (dindindin), sannan itace abu na biyu dake haifar da makanta.
Akan dambarwa dake faruwa a Nijar, mun samu tattaunawa da jakadan Nijar din anan Amurka, Mamadou Kiari Liman-Tinguiri, mun kuma duba taron gaggawa da Kungiyar ECOWAS ta yi a Abuja, Najeriya, da wasu rahotanni.
A hirarsa da Muryar Amurka, Jakadan Nijar a Amurka, Mamadou Kiari Liman-Tinguiri, ya ce duk da'awar yin wannan kasada ta juyin mulki ba ta da wata hujja ko kadan.
Kungiyar Super Falcons wacce ita ce ta 40 a iya taka leda a fagen wasan kwallon kafa na mata a duniya, ba ta sha kaye ko daya ba a wasannin da ta buga, yanzu kuma ta doshi zagayen kwaf-daya.
Halin matsin tattalin arziki a Najeriya sakamakon cire tallafin man fetur ya sa hukumomin yin kokarin bunkasa amfani da wasu hanyoyin makamashi da ba na fetur ba, abin da ya hada da canza injuna zuwa masu aiki da iskar gas da fadada tashoshin cajin motoci masu amfani da lantarki, da wasu rahotanni
Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da kokawa da tsadar kayan masarufi, a makon jiya 'yan majalisar dokokin kasar suka amince da bukatar shugaba Bola Tinubu ta ciyo bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya don taimakawa wajen rage radadin cire tallafin man fetur, da wasu rahotanni
Illolin matsalar wutar lantarki a Najeriya ba su tsaya kawai ga hana ci gaban tattalin arziki ba, har ma da bangaren kiwon lafiya; haka kuma hukumomin Ghana su na shirin kaddamar da wata tashar samar da wutar lantarki daga hasken rana da aka gina akan madatsar ruwa da wasu rahotanni
A makon da ya gabata ne Kotun Kolin Amurka ta yanke hukuncin hana amfani da tsarin ware wasu guraben daukan dalibai a jami’o’i bisa launin fatar dalibai, da wasu rahotanni
A Najeriya, talauci shi ne babban dalilin da ke sa yara da dama ba sa zuwa makaranta, sai dai ana kara kokarin ganin an magance wannan matsala, yadda Musulmai suka gudanar da Idin babbar Sallah, da kuma wasu rahotanni
Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun bukaci hukumomin Najeriya da su dakatar da shirin mayar da ‘yan gudun hijira garuruwansu a arewa maso gabashin kasar, da wasu rahotanni
Yajin aikin da masu dafa abinci a makarantu ke yi na iya tilasta wa yaran makaranta da ke cin gajiyar shirin ciyar da dalibai da gwamnatin Ghana ta bullo da shi zama da yunwa, da wasu rahotanni
Tun bayan ayyana cire tallafin man fetur kawunan ‘yan Najeriya ya rarrabu, yayin da wasu ke goyon baya, wasu na sukar matakin, saboda su na ganin zai shafi da dama daga cikin marasa galihu da ke fama da matsin tattalin arziki, da wasu rahotanni
A jawabinsa na farko jim kadan bayan rantsar da shi da aka yi, sabon shugaban Najeriyar Bola Tinubu ya bayyana cewa za a soke tallafin man fetur da gwamnati ta kwashe shekaru da dama ta na bayarwa, da wasu rahotanni.
A cewar wata kungiyar kasa da kasa mai zaman kanta da ake kira ONE, a 2021, yawan bashin da ake bin kasashen Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 644.9. Kungiyar ta kara da cewa a karshen wannan shekara ta 2023, kasashen Afirka za su biya dalar Amurka biliyan 68.9 na basussuka, da wasu rahotanni
Wani mazaunin jihar Kano a Arewacin Najeriya wanda a baya ya yi ta’ammali da miyagun kwayoyi, yanzu ya tuba, kuma har ya shiga taimakawa sauran masu ta’ammali da miyagun kwayoyin don ganin su ma sun daina, da wasu rahotanni
Shirin Taskar VOA na wannan makon, zai duba irin matakan kariya da ya kamata a dauka yayin da hukumar kula da yanayi a Najeriya ta yi hasashen samun mummunan ambaliyar ruwa a damunar bana
Domin Kari