Albarkacin ranar yaran Afrika ta bana, kungiyoyin kare hakkin yara kanana a Nijar sun gargadi mahakunta akan samar da daidaito tsakanin yaran kasar ta yadda ‘ya'yan masu karamin karfi zasu samu makamanciyar damar da ‘ya'yan attajirai da na manyan ma’aikata ke da ita a makarantun boko.
Hukumomin mulkin sojan jamhuriyar Nijar sun tsaurara matakai da nufin taka burki ga masu amfani da nufin saka tsari a kafafen sadarwa bayan da suka ce wasu na fakewa da wadanan hanyoyi don cin zarafin mutane.
A yayinda aka fara samun saukar ruwan sama a albarkacin damunar bana a sassan jamhuriyar Nijar, hukumar kula da aiyukan agajin gaggawa ta sanar cewa ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mutane fiye da 10 yayin da daruruwan gidaje suka ruguje
An yi bikin kaddamar da ayyukan kwashe sojojin Amurka a hukumance da yammacin ranar Jumma’a a filin jirgin sojan sama da ke birnin Yamai na Jamhiriyyar Nijar.
Kasar Amurka ta sanar da ware karin miliyoyin dala domin tallafa wa al’umomin da ke bukatar agaji a kasashen yammacin Afrika.
Wata tawwagar mataimakin ministan tsaron kasar Rasha hade da ta ‘yan kasuwar Rashar sun kai ziyara a jamhuriyar Nijar inda suka gana da hukumomin mulkin sojan kasar a ci gaba da karfafa hulda a sabon kawancen da kasashen 2 suka kulla a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
A ci gaban rikicin diflomasiyar da ke tsakanin hukumomin Nijar da na jamhuriyar Benin, Shugaban Majalisar Sojoji ta CNSP ya ki ganawa da Ministan Ma’adinan Benin a wani taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin man fetur da ya hada jami’an kasashen 2 a birnin Yamai.
A jamhuriyar Nijar wani gidan talabijan mai zaman kansa wato Canal 3 Nijar ya kori ma’aikata sama da 30 bayan da suka tsunduma yajin aikin kwanaki 3 a makon da ya gabata.
Lamarin ya faru ne da la’asar ta ranar Litinin 20 ga watan Mayun 2024 lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai harin ta’addanci kan sansanin soja a kauyen Boni na gundumar Makalondi da ke tsakanin iyakar Nijer da Burkina Faso.
Wata tawagar jami'an gwamnatin Amurka ta isa Jamhuriyar Nijar da daftarin da ke dauke da fasalin da Amurka ke fatan ganin an yi amfani da shi wajen kwashe dakarunta daga Nijar kamar yadda hukumomin mulkin sojan CNSP suka nuna bukata a watan Maris din da ya gabata.
Gwamnatin rikon kwarya ta Jamhuriyar Nijar ta maida martani bayan da shugaban kasar Benin Patrice Talon ya dauki matakin hana lodin danyen man da Nijar ke shirin fara shigarwa kasuwannin duniya a tsakiyar watan Mayu.
A watan Mayu ne ya kamata a fara jigilar danyen man Nijar daga tashar jirgin ruwan Seme a jamhuriyar Benin zuwa kasuwannin duniya, gwamnatin shugaba Patrice Talon ta yanke shawarar hana gudanar da wadannan ayyuka da nufin maida martani ga mahukuntan Nijar da ke ci gaba da rufe iyakar kasar.
Rukunin sojojin Rasha na biyu ya isa jamhuriyar Nijer wadanda aka ayyana a matsayin masu aikin horo a ci gaba da karfafa huldar aiyukan soja a tsakanin kasashen biyu bayan juyin mulkin da ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.
A yayin da kasashen duniya ke bukukuwan karrama ranar ‘yancin aikin jarida a yau 3 ga watan Mayu, rahotanni na nuni da cewa ‘yancin aikin jarida da ‘yancin fadin albarkacin baki na fuskantar barazana a kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso.
Jami’an Amurka sun fara tantaunawa da shugabanin Majalissar CNSP mai mulkin Nijar da nufin tsara aiyukan ficewar dakarun Amurka 1,100 da ke girke a jihar Agadez yau shekaru sama da 10 a wani bangare na karfafa matakan yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
An cimma wata yarjejeniyar da a karkashinta jamhuriyar Nijar ta amince ta sayar wa kasar Mali lita million 150 na man diesel akan farashi mai sauki.
Domin Kari