Batun sauya fasalin kudin Najeriya da babban bankin kasar ya ce zai yi yana ta janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin kungiyoyi masu zaman kansu da ma manazarta a harkokin kudi, musamman ma akan lokacin da bankin na CBN ya bayar.
Babban Bankin Najeriya ya ce zai sake fasalin manyan takardun kudi na Naira ya zuwa ranar 15 ga watan Disamba na wannan shekarar. Kudaden su ne Naira 200, da 500 da kuma Naira 1000 daya.
Najeriya tana daga cikin kasashen da a 'yan shekarun nan ke fama da matsalar ruwa, na noman rani ko wanda al'umma za su yi aiki da shi kamar sha ko ayyukan yau da kullum.
Kwamitin Majalisar Dokokin Najeriya kan sake gyara Kundin tsarin Mulkin kasar na 1999, ya zargi gwamnonin jihohi 25 da yin katsalandan tare da kawo cikas ga shirin samar da sabon kundin tsarin mulki a kasar.
Shugaban zai gabatar da kasafin kudin na 2023 a gaban Majalisar Dokokin kasar, wanda zai kai Naira triliyan 19.7, hakan na nufin an samu karin Naira triliyan 2 tsakani da kasafin kudin bana da zai kammala a watan Disamba.
A Najeriya, Hukumar Wayar da kan Al'umma da hadin gwiwar Ma'aikatar Kula da ayyuka na musamman sun kaddamar da wata kungiya wacce za ta aiwatar da kudurin mata a fanoni daban daban, kama daga Siyasa, zaman lafiya da tabbatar da dogaro da kansu.
Majalisar dattawa Najeriya ta kasa daukar matsaya kan wa'adin makwanni 6 da ta bai wa Shugaba Mohammadu Buhari kan ya dauki kwararan matakai akan sha'anin tsaro ko kuma ta tsige shi, a maimakon haka ta mayar da hankali ne akan shirin kasafin kudin badi.
Majalisar zartarwa ta Najeriya ta amince da kashe Naira Miliyan 718 don ayyukan tsaro da sa ido kan harkokin sufurin jiragen kasa na Abuja.
Da alamar dai har yanzu matsalar nan ta rashin bin ka'ida da kuma tsautsayi na ci gaba da addabar bangaren gine gine a Najeriya, inda aka sake gamuwa da hadarin faduwar gini a Abuja, inda wasu mutane su ka mutu, wasu kuma su ka ji raunuka.
Daga dukkan alamu an sami rudani a kan yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ke kashe kudade kan tallafin man-fetur, har ya sa Majalisar Wakilai kafa Kwamitin wucin gadi domin ya yi bincike a kai.
Domin Kari