Shirin ya mafia hankalo kan kafewar jinin al’ada na mata wato menopause da kuma daukewar sha’awa da kwayoyin haihuwa a maza wato Andropause.
Ana danganta kafewar jinin haila wato menopause da yawan jin zafi, gumi, yawan fushi da kuma sauyin lokacin saukar jinin al’ada. Andropause anayi ne da ake masa la’abi da “menopause din maza” wanda kehaifar da gagarumin sauyi a yanayin daidaituwar sinadarin hormones da kuma lafiyar jikin maza.
Kimanin yara miliyan ashirin ne aka kiyasta ba sa zuwa makaranta a Najeriya wani lamari da kwararru suke ta’allakawa akan matsalolin al’adu, da tattalin arziki da kuma rashin makarantu na kwarai da wa su rahotanni
Shirin lafiyarmu na wannan makon, ya mai da hankali akan cututtukan Kansar da suka fi addabar mata a fadin duniya.
Hukumar Lafiya Ta Duniya ta sahalewa sabon maganin rigakafin zazzabin cizon sauro. Ana fatan za a gaggauta fitar da sabon maganin a kasashen Afirka a cikin watanni masu zuwa.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutane dubu dari shida da tamanin da biyar ne suka rasa rayukan su a dalilin cutar kansar mama a shekarar 2020 a fadin duniya. Hukumar ta ce an gano wasu mata miliyan 2.3 dauke da cutar ta cancer cikin wannan shekarar.
Wasu daga cikin kurakuren da marasa lafiya ke samu a wajen duba lafiyarsu a Najeriya, ana danganta su ne da rashin kwarewar jami’an lafiya ko kuma shagunan magani na cikin unguwa, da wasu rahotanni
Domin Kari