Jumahuriyar Nijar ta sake bude kan iyakokinta da wasu makwabtanta, mako guda bayan juyin mulkin da ya girgiza yankin Sahel na yammacin Afirka.
‘Yan Nijar mazauna kasashen ketare sun bayyana fargaba tare da kira ga kungiyar ECOWAS da sauran kasashen duniya da su yi duk mai yiwuwa wajen dawo da zaman lafiya a kasarsu.
Hakan ya biyo bayan matsayar da kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS ta cimma na cewa za ta dauki matakin soji idan har dakarun da suka yi juyin mulki a Nijar ba su mayar da kasar kan turbar dimokradiyya ba.
Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta bukaci 'yan kasarta da ke Nijar da su karbi tayin da hukumomin Faransa suka yi musu na shiga jiragen da za su kwashe mutane a ranar Talata, kwanaki bayan da sojoji suka kwace iko a kasar da ke yammacin Afirka.
A yayin da gwamnatin Faransa ta ayyana shirin kwashe ‘yan kasarta daga Nijar, kasashen Mali da Burkina Faso sun jaddada goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar.
Adadin wadanda suka mutu sakamakon wani kazamin harin kunar bakin wake da aka kai kan wani gangamin zabe na wani limamin kungiyar Taliban ya haura zuwa 54 a yau Litinin, yayin da Pakistan ke gudanar da jana'izar kuma Gwamnati ta sha alwashin zakulo wadanda suka kai harin.
Rundunar sojan Nijar da ta kwace mulki a makon da ya gabata tare da hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum, ta zargi gwamnatin hambararren shugaban kasar da bai wa Faransa izinin kai hari akan fadar shugaban kasar domin kokarin kubutar da Bazoum.
Jam’yar PNDS Tarayya madugar kawancen jam’iyun hambarariyar gwamnatin Nijar ta musanta zargin hannun tsohon Shugaban kasa Issouhou Mahamadou, a juyin mulkin da soja suka yi wa Mohamed Bazoum a ranar Larabar ta gabata.
Halin matsin tattalin arziki a Najeriya sakamakon cire tallafin man fetur ya sa hukumomin yin kokarin bunkasa amfani da wasu hanyoyin makamashi da ba na fetur ba, abin da ya hada da canza injuna zuwa masu aiki da iskar gas da fadada tashoshin cajin motoci masu amfani da lantarki, da wasu rahotanni
Sojojin da suka kifar da shugaba Mohamed Bazoum a ranar Larabar da ta gabata a Jamhuriyar Nijar sun zabi kwamandan rundunar tsaron fadar Shugaban kasa General Abdourahamane Tchiani a matsayin shugaban majalissar CNSP domin ya jagoranci al’amuran kasar.
Wasu masu zanga-zangar goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a kasar sun yi kaca-kaca da ofishin jam’iyar PNDS mai mulki a yau Alhamis tare da kwasar ganima da farfarsa gilasai da kona gomman motoci.
Bangarorin siyasa a Jamhuriyar Nijar sun fara maida martani bayan da wasu sojoji suka ba da sanarwar kifar da shugaba Mohamed Bazoum daga karagar mulki a ranar Laraba 26 ga watan Yuli, yayin da jam’iyar PNDS mai mulki ke cewa za ta yi gwagwarmaya don mayar da hambararen shugaban akan kujerarsa.
A ranar Alhamis ne rundunar sojojin Nijar ta bayyana goyon bayanta ga juyin mulkin da sojoji masu tsaron fadar shugaban kasar suka yi, inda rundunar ta ce abin da ta sa a gaba shi ne kaucewa ta da zaune-tsaye a kasar.
Shugaba Ahmed Bola Tinubu ya mika sakon fatan alheri ga 'yan wasan kwallon Najeriya na Super Falcons yayin da suke shirye-shiryen karawa da Australia a wasansu na biyu na rukuni a gasar cin kofin duniya ta mata na FIFA da ke gudana a Australia da New Zealand 2023.
Duk da cewa wasu dattawa karkashin kungiyar hadin kan Arewa, Northern Alliance Committee sun nuna goyon baya ga tsare-tsaren gwamnatin Bola Tinubu, dattawan sun mika bukata cewa ya mayar da hankali wajen fitar da shirin rage radadin cire tallafin man fetur.
Majalisar Dokokin Ghana ta kada kuri'ar soke hukuncin kisa, wanda ya sa kasar ta kasance ta baya-bayan nan cikin jerin kasashen Afirka da dama da suka yi yunkurin soke hukuncin kisa a shekarun baya-bayan nan.
Domin Kari