A yau Litinin, fadar Kremlin ta yi Allah-wadai da kisan Shugaban Hizbullahi Hassan Nasrallah da hare-haren Isra’ila ta sama su ka yi a makon da ya gabata sannan tace tana da hasashe mai karfi dake nuna yiyuwar fadadar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Hezbollah na riko ya sha alwashin ci gaba da yakar Isra’ila sannan ya bayyana cewar a shirye kungiyar take ta shafe dogon zango tana yaki duk kuwa da cewar an hallaka manyan kwamandojinta, ciki harda jagoranta, Hassan Nasrallah.
Gabanin fara bukukuwan murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kan Najeriya karo na 64, rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayyar Najeriya tace ta tura wadatattun jami’ai da kayan aiki zuwa lungu da sako na garin Abuja.
Najeriya ta yi kira ga MDD da ta bayar da fifiko ga neman yafewa kasashe masu tasowa basussuka ta kuma bukaci a ba ta kujera ta dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar; Mutanen da ambaliya ta lalatawa gidaje a Maiduguri suna zargin hukumomi da tashisu daga gine-ginen gwamnati, da wasu rahotanni
Shugaba Vladimir Putin ya gargadi Amurka da kawayenta akan cewar Moscow na duba yiyuwar maida martani da makaman nukiliya matukar suka bari Ukraine ta kai hari cikin Rasha ta hanyar amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango da aka kera a kasashen yammacin duniya
Guguwa Helene da ta ratsa jihohin Florida da Georgia cikin daren Juma’a na da ya daga cikin irinta mafi karfi da aka gani a tarihin Amurka, inda ta hallaka mutum guda tare da haddasa ambaliyar ruwa a unguwanni da katse wutar lantarki ga fiye da gidaje da kantuna miliyan biyu
A yau Alhamis, Isra’ila ta yi fatali da shawarar tsagaita wuta tsakaninta da Hezbollah, inda ta bijirewa kawayenta ciki har da Amurka da suka bukaci a dakatar da yaki nan take na tsawon makonni uku domin bada damar yin amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen kaucewa fadadar yakin
Domin Kari