A jawabinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kamfanin a matsayin abin alfahari wajen ci gaban tattalin arziki da saka jari a kasar.
Fadar shugaban Najeriya ta bayyana kamfanin takin na Dangote a matsayin mafi girma a duniya.
Jama'a da dama na nuni da yadda matsaloli suka yi wa kasar katutu, kama daga batun karancin man na fetur da kuma rashin wutar lantarki.
Darakta a hukumar bada agajin gaggawa ta nema Alhaji Bashir Garga yace yan Najeriya 450 ne suka dawo gida Najeriya ta filin jiragen sama na Abuja.
A yayinda ya rage shekara daya a gudanar da Babban zaben kasa a Najeriya yanzu haka hankulan magoya bayan jamiar dake mulki a Najeriya ta APC ya koma yankin kudanci kasar.
Wani alkalin babbar kotun jihar lagos, Hakeem Oshodi ya zartar da hukuncin daurin rai da rai akan gawurtaccen mai garkuwa da mutanen nan na birnin Lagos Chukwudimeme Onwuamadike da akafi sani da suna Evans.
A karshen wata ziyara ta kwanaki uku da ta kawo Najeriya, mataimakiyar sakatatiyar harkokin wajen Amurka mai kula da nahiyar afrika Madam Akunno Cook ta jaddada kudirin kasar Amurka na tallafawa Najeriya samun nasara a fannonin kirkire kirkiren fasahar zamani da Finafinai domin cigaban kasa.
Duk da gargadin da jami’an tsaro suka yi na hana taruwa a Lekki, hakan bai hana daruruwan matasa fitowa a ranar Laraba domin tunawa da wannan rana ba.
Gwamnatin jihar Lagos ta kafa dokar hana makiyaya kiwo a jihar sakamakon wata doka da gwamnan jihar Mr Babajide Sanwo Olu ya rattawabawa hannu.
A yayinda ake kira ga gwamnatin Najeriya data dauki matakin hana daukan fansa da wani mai kiran kansa mai kare yancin Yarbawa Sunday Ighaho ke yi na farma Fulani, yayinda shugabannin Hausawa da Fulani na kudancin kasar su ka dukufa wajen yin kira ga makiyaya su guji daukan doka a hannunsu.
Shugabannin Fulani da sauran masu fada a ji a yankin Yammacin Najeriya sun yi Allah wadai da wa’adin da Sunday Adeyemo Igboho wani mai ikirarin kare yankin Yarbawa da ‘yan sanda ke nema ya bai wa dukkan Fulani makiyaya mazauna jihohin yarbawa wa’adin ficewa daga yankin kafin ranar Litinin.
Yanzu haka ‘yan Najeriya, musanman al’ummar Yarbawa, na ci gaba da maida martani game da ganawar da sarkin Fulanin yanmacin Najeriya, Alhaji Muhammadu Babbado, ya yi da karamar jakadiyar ofishin Jakadancin Amurka a Legas. A yayinda wasu ke yabawa da ganawar, wasu kuwa na ganin bai dace ba.
A wani mataki da Babban Bankin Najeriya ya ce zai taimaka ma 'yan Najeriya masu harka da dala, musamman masu turo dalar Amurka zuwa gida Najeriya, an bullo da wani tsarin turo kudi tare da biyan Babban Bankin kamasho.
Yanzu haka dai farashin dabbobi da sauran kayan abinci sun yi tashin gwauron zabi a Legas da sauran jihohin yammacin Najeriya sakamkon yajin aikin da ‘yan kasuwa na wannan bangare suka fara.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta gargadi masu shirin sake gudanar da zanga zangar ENDSARS a Legas da su shiga taitayin su, bayan da wasu suka yi barazanar sake shiga zanga zangar da ta haifar da cece-ku-ce a baya a kan yanda ‘yan sanda suka yi amfani da karfin tuwo kan masu zanga zangar.
Kwanaki 5 bayan sace wasu daliban makarantar sakandare da ‘yan bindiga su ka yi a garin Kankara da ke jihar Katsina, wasu jihohin arewacin Najeriya sun dauki matakin rufe makarantunsu. Sai dai jama’a da sauran masana harkokin ilimi na ganin wannan tamkar bada kai ne ga ‘yan ta’adda a kasar.
‘Yan Najeriya na ci gaba da yin tsokaci bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya amince zai bayyana a gaban Majalisar Dokokin kasar.
Ranar 9 ga watan Satumban kowace shekara na zama ranar da majalisar dinkin duniya ta ware domin bikin bada kariya ga ilimi, da makarantu, da dalibai daga bala’o’i dabam daban da suka hada da ta’addanci.
Domin Kari