Dakarun Afirka ta Yamma sun ce sun kwato mutane fiye da 5000 wadanda 'yan Boko Haram suka tsare su a wasu kauyuka a wani hari da suka kai wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mayakan Boko Haram 60 a iyakar Najeriya.
Daga karshe Cocin Anglica ta Australia ta nemi gafara inda ta ce abin kunya ne da kuma takaici da bayan rahoton da ya nuna cewa akalla mutane fiya da 1100 ne suka kalubalanci cocin akan yin lalata da su cikin shekaru 35 da suka gabata.
Bangladesh: ‘Yan sanda sun yi amfani da yaji mai sa hawaye akan masu zanga zangar dake adawa da karin kudin mai, bayan da boren ya juye ya koma tarzoma.
Nigeria: Wasu ‘yan mata hudu sun kai harin kunar bakin wake inda suka kashe mutane biyu kana suka raunata wasu 16.
A kasar Habasha, gocewar laka a wata dalar shara ta halaka akalla mutane 46, wasu da dama kuma sun bace, a wani wuri dake wajen Addis Ababa babban birnin kasar.
Park Geun-Hye Ta Bar Gidan Gwamnatin Koriya Ta Kudu Blue House
A wannan bidiyo, Khalifa Aliyu Ahmad Abulfathi zai yi bayani kan mummunar akidar kungiyar Boko Haram da irin ta’asar da suka yi a lokacin suna ganiyar kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya.
Najeriya: Shugaba Muhammadu Buhari ya koma gida bayan hutun jinya na kusan watanni biyu a Burtaniya.
An Tabbatar Da Tsige Shugabar Korea ta Kudu Park Guen-hye
A wannan bidiyo za ku kalli yadda ‘yan kungiyar Boko Haram suke gudanar da atusaye da motsa jiki a wani yankin arewa maso gabashin Najeriya da suka karbe ikonsa a lokacin suna ganiyar cin karensu ba babbaka a tsakanin shekarun 2014 da 2015. A yi kallo lafiya.
A wannan hira da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya yi da Muryar Amurka, ya bayyana irin nasarar da aka samu akan kungiyar Boko Haram tun bayan da gwamnatin shugaba Muhamamd Buhari ta karbi ragamar mulki tare da bayyana irin kalubalen sake gina yankin dake gaban gwamnatin jiha da ta tarayya.
Domin Kari