Afghanistan: ‘Yan ta’adda dauke da makamai da suka yi shigar likitoci sun kai hari a wani asibitin soji dake Kabul inda suka kashe akalla mutane 30 suka kuma jikkata wasu da dama.
Ivory Coast: Dam din Soubre da China ta gina zai rage gibin karancin wutar lantarkin da ake samu a kasar yayin da ake sa ran zai fara aiki a karshen watan Maris.
A wannan bidiyo, za ku kalli fatawar da Sheikh Duguri ya bayar kan ma’anar kalmar jihadi, inda ya nuna cewa irin jihadin da ‘yan kungiyar Boko ke ikrarin suna yi ya sabawa koyarwar addinin Islama.
Muryar Amurka ta leka wani sansanin ‘yan gudun Hijira dake garin Bama da ya yi fama da hare-haren kungiyar Boko Haram. A wannan bidiyo za ku kalli yadda yara ke zuwa makaranta da kuma yadda ake kokarin samar da ababan more rayuwa a wannan sansanin.
Nigeria: Tawagar kwamitin sulhu na MDD ta ziyarci sansanin ‘yan gudun hijirar wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita a Maiduguri.
Somalia: Matsalar Fari a kudancin Somali ta kashe akalla mutane 110 cikin kwanaki biyu.
Lokacin da Muryar Amurka ta ziyarci garin Bama dake Jihar Maiduguri, mun zanta da wasu mazauna garin inda suka mana bayani kan yadda ‘yan kungiyar Boko Haram suka rika harbi tare da jefa mutane cikin ruwa daga kan Gadar Bama a lokacin suna rike da ikon garin.
Turkey: Dakarun Turkiyya suna kokarin rufe bakin iyaka da Siriya da Katanga da bama-bamai da aka binnewa karkashin kasa, yayin da ake ci gaba da fada da kungiyar IS.
A wannan karon za ku kalli yadda kungiyar Boko ta ke kai hare-hare a duk lokacin da ta bushi iska, a yankin arewa maso gabashin Najeriya a tsakanin shekarun 2014 da 2015, kamar yadda hoton bidiyo da suka dauka da kansu ya nuna.
Majalisar Dinkin Duniya ta fara raba abinci a Sudan ta Kudu
Yakin neman kwato Mosul da aka fara a watan Oktoba na ci gaba da tilastawa mutane ficewa daga gidajensu.
A ci gaba da kawo maku faya-fayen bidiyon ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram, tsarabarmu ta yau ta kunshi yadda kungiyar ta ke shirya farfagandarta. A yi kallo lafiya.
Ana Bikin Gargajiya a Kasar Angola
Isra’ila Na Rushe Gidajen Da Aka Gina Ba Bisa Ka’ida Ba a Yankin Falasdinawa
A wannan bidiyo za ku kalli hirar wasu makiyayi da Muryar Amurka inda suka ba da labarin yadda suka gujewa yankunansu saboda addabarsu da ‘yan kungiyar Boko Haram ke yi da sace-sace shanu a garinsu na Dar Gemal.
Domin Kari