ZIMBABWE: A Zimbabwe al’umar kasar sun gwammace amfani da kudin Bitcoin da ake amfani da su wajen saye da sayarwa ta Internet, maimakon kudaden kasar saboda tsaananin hauhawar farashi da kayyade kudi da Bankuna suka yi, wadda warwas ya maida mudaden kasar tamkar ganyen itace.
Shugabannin Addini da Na Kungiyoyin Matasa Sun Kalli Majigin VOA Akan Boko Haram a Abuja.Wadanda suka kalli majigin sun hada da Shaikh Abdullahi Bala Lau shugaban IZALA da Rabaran Musa Asake, sakataren kungiyar kiristocin Najeriya.
NIGER: Dakarun rundunar G5 Sahel, wadda ta kunshi kasashen Burkina Faso da Chadi, Mauritania da Niijer ta kaddamar da matakin soja na farko tareda goyon bayan sojojin kasar Faransa
Shuwagabannin duniya ciki harda na Amurka, Donald Trump, da na kasar Sin Xi Jinping, da na Rasha Vladimr Putin sun isa birnin Danang wajan taron koli na tattalin arzikin kasashe dake yankin Asiya da Pacific.
Malamai Da Iyaye Sun Yi Zanga-zanga
Daga karshe kuma a Afrika ta Kudu wata kungiyar mai kulla da bayarda gapapun mutane kiyauta , ta ce ta na fuskantar karacin gapapuwan yayinda ta gudanarda dashe kasa da 400 a shekara, yayinda mutane fiye 4300 na bukatar a yi musu dashe.
A kasar Columbia 'yan sanda sun kama tan 12 na hodar iblis kamu mafi girma a tarihin kasar, ana danganta miyagun kwayoyin ga wata alummar kasar da suka yi kaurin suna wajen miyagun ayyuka.
Masu Kula Da Harkokin Tsaron Amurka Da Nijer Sun Gudanar Da Taron Kwamitin SGI
A Amurka 'Yan jam’iyyar Democrat sun lashe mukamai da yawa a jihar Virginia, da New Jersey, da New York da sauran jihohi, a babban zabe na farko da aka yi tun bayan nasarar da shugaban kasa Donald Trump yayi, shekara daya da ta gabata.
Shugaban ‘yan adawar kasar Kenya, Raila Odinga, ya ce yana bukatar gwamnatin hadin guywa ta rike kasar har zuwa watanni 6 yayinda za a duba kundin mulkin kasar don rage karfin ikon shugaban kasa.
Shirin da aka kirkiro na musamman don baiwa matasa damar bayyana ra'ayoyinsu game da abubuwan da suka shafesu.
Gwamnatin Saudiyya tace Lebanon ta ayyana yaki saboda abunda ta kira takala daga kungiyar Hezbollah.
A wani harin da wasu mata hudu suka kai a Unguwar Landan da ke Kaleri,a wajen Birnin Maiduguri ranar talata, mutane shida sun jikkata.
Kungiyar likitoci ta Doctors without Borders ta ceci mutune kusan dari shida da suka yi yunkurin ketara tekun medatarenia a kwale-kwalen roba daga Libia.
SYRIA: Jami’an gwamnati sun sake kwace birnin Deir mai arzikin man fetur daga hannun ‘yan kungiyar ISIS.
Domin Kari