Shugaban Sudan ta kudu Salva Kiir na ziyarar kwanaki biyu a kasar Sudan da zummar warware takaddamar bakin iyaka da ta addabi kasashen biyu, da kuma duba yadda kasashen zasu gyara dangantakar da ke tsakaninsu.
‘Yan adawa dake zanga zangar sun kara da yan sanda a unguwar Kawamgware dake birnin Nairobi sa’o’i kafin a bada sakamakon lashe zabe da shugaba Uhuru Kenyata yayi a maimaitawar zaben mai cike da rigingimu kuma ana ci gaba zanga-zanga a duk fadin birnin Nairobi.
A Isra’ila kuma, yahudawa sun rushe wata hanyar ‘yan fasa kwoiri ta karkashin kasa dake a ta kan iyyaka da Gaza, suka kashe akalla mutane 7.
Ministan Cikin Gidan Nijar Bazoum Mohamed ya bayyana sakamakon hasarar da aka samu a taron gangamin da wasu kungiyoyin fararen hullar Nijar suka shirya a jiya Lahadi wacce ta rikide ta koma zanga-zanga,
An fara horar da sabbin kurata na soja su fiye da 6,000 a sansanin soja dake birnin Zaria a arewacin Najeriya, a matsayin wani bangaren hadin guywa da rundunar sojan Burtaniyya.
Dubban mutane sun yi gangami akan titunan Yongon jiya Lahadi, don nuna goyon bayansu ga dakarun kasar, wadanda suka sha suka daga kasashen duniya saboda farmakin da ta kai kan musulmin Rohingya dake kasar.
Wani alkali a Afrika ta Kudu ya yanke hukunci ga wasu matasa fararen fata ‘yan shekaru 19 da 16 , na daukar hoton bidio kansu suna tursasa wa wani bakar fata shiga cikin Makara kana suna barazanar kona shi.
Shugaban kasar Amurka Donaled Trump ya bada izinin wallafa takardun bincike har 2,800 dake da alaka da kisan da aka yiwa tsohon shugaban Amurka John F. Kennedi amma ya hana bada wasu daga cikin su, domin ci gaba da bincike.
Ministan kudin kasar Afrika ta Kudu Malusi Gigaba yace kasar na fuskantar bashii mai tarin yawa wanda ke kara haifar da gibi da koma baya ga tatillin arzikin kasar,
Gwmanatin Nijar ta tattauna da shuwagabanin makarantu masu zaman kansu na kasar a wani mataki na kawo tsari kan yadda makarantun ke gudanar da ayukansu .Yahouza Saddissou shine Ministan ilimi mai zaurfi na kasar ya kuma yi karin bayani.
Shuwagabanin Ecowas sun kara jaddada anniyar cigaba da shirin fitarda kudaden bai daya da suka kudirta soma amfani da su a shekarar 2020
Domin Kari