Sabon Jakadan Najeriya, A Amurka Honorable Justice Sylvanus Adiewere Nsofor, ya isa kasar Amurka domin kama aiki, ya nuna farin cikin sa a lokacin liyafar da aka shirya masa a ofishin jakadancin Najeriya dake Amurka.
Libya: Gwamnati ta sha alwashin gudanar da bincike akan zargin cinikin bayi bayan an saki wani hoton bidiyo dake nuna yadda ake cinikin ‘yan ci rani da masu gudun hijira
U.S: Jiya lahadi dubban jama’a sun yi tattaki a birnin Washington DC daga dandalin da ake kira national mall zuwa majalisa inda suka bukaci a tura Karin tallafi ga wadanda mummunar guguwar nan da aka yiwa lakavbin Maria ta shafa a Puerto Rico.
Nigeria: Wani kampani mai tasowa yana amfani da tsoffin firinji don sauyasu zuwa na’ura mai amfani da hasken rana na adana abinci kada su gurbace, don taimakawa ‘yan kasar da ke fama da rashin wutar lantarki
Jami’an bada agajin gaggawa da wasu ‘yan kungiyar Civilian JTF sun ce wasu ‘yan kunar bakin wake su hudu sun kashe mutane 10, sun kuma jikkata kusan mutane 30 a Maiduguri.
Rahotannin na nuna cewa Shugaba Robert Mugabe dan shekaru 93 ya ki ya amince da kokarin da sojan kasar keyi na sauke shi daga mukaminsa, biyo bayan juyin mulkin da aka yi a kasar ranar Laraba.
Sojoji da motocinsu sun toshe hanyoyin shiga ko fita daga ofisoshin gwamnati a birnin Harare, yayin da suka karbi ragamar kasar da tun 1980 shugaba Robert Mugabe yake mulkinta, duk da dai sun ce ba juyin mulki suka yi ba.
Sakataren harkokin wajen amurka Rex Tillerson yayi kira ga gwamnatin Myanmar akan ta kare hakkokin bil’adama ta kuma gudanar da sahihin bincike akan rahotannin keta hakkin bil’adama akan musulmin Rohingya.
Wata gidauniya tana koya ma nakasassu sana'o'i dabam-dabam tare da samar musu da jari na gudanar da wadannan sana'o'i bayan sun koya
Kenya: Kotun Kolin Kenya tana nazarin korafin da aka gabatar dake kalubalantar lashe zaben da Shugaba Uhuru Kenyatta yayi a zaben shugaban kasa da aka sake a watan da ya gabata
Iran: Shugaba Hassan Rouhani ya isa yankin da girgizar kasa mai karfin maki 7.3 ta hallaka mutane 450 kuma yace gwamnatinsa zata taimaka iya kokarinta.
Domin Kari