Netherlands: A Netherlands, Wasu Alkalai a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, sun wanke tsohon shugaban Ivory Coast, Laurent Gbagbo daga zargin aikata laifukan yaki, inda suka nemi da a sake shi ba tare da bata lokaci ba, lamarin da ya sa masu goyon bayansa suke ta murna a birnin Abidjan.