Shugaban Amurka Joe Biden, ya ce ba zai dage takunkumin tattalin arziki da aka kakabawa kasar Iran ba, har sai Tehran din ta rage yawan aikin bunkasa sanadarin Uranium din ta, kamar yadda aka cimma, a yarjejeniyar kasa-da-kasa ta 2015, wanda aka yi, don hanata hada makaman, na kare dagi.