Masu yawon bude ido suna ficewa daga Gambia yayin da Shugaba Yahya Jammeh ya kafa dokar ta baci ana gab da rantsar da abokin hamayyarsa Adama Barrow.
Malaman jami'ar Zinder dake Damagaram sun sake shiga wani yajin aiki game da bukatunsu da gwamnati ba ta biya na albashinsu.
Akalla mutane uku suka mutu kana wasu 15 suka jikkata a wani harin kunar bakin wake a farfajiyar wata jami’a dake arewa maso gabashin Najeriya
Hukumomin Turkiyya sun kama Abdulkadir Masharipov, mutumin da ake zargi da kashe mutane 39 ranar sabuwar shekara a wani gidan rawa dake Istanbul.
Gwamnatin Nijar ta bayyana cewa, tana bukatar kudadan da suka kai dala Milliyan 271, domin gudanar da ayyukan jin kai a yankunan da suka fuskanci matsaloli daban-daban kamar ambaliyar ruwa da karancin abinci da matsalar Tamowa da ta annoba da kuma matsalar da ta shafi 'yan gudun hijira.
Shugabani daga kasashen afrika 30 da kasar Faransa, sun gana a babban birnin Bamako, inda ake shirin tattaunawa akan yaki da 'yan ta’adda da kuma kara daidata demokadiya a kasar
Gwamnatin Shugaba Barak Obama ta kawo karshen tsarin ba ‘yan asalin kasar Cuba izinin zama a Amurka da zarar sun shiga kasar ba tare da bisa ba.
Ma'aikatar kiwon lafiyan Nijar ta yi kiran hadin kai domin bunkasa fannin.
Hira Ta Musamman Tare Da Malam Nick Dazan, Daraktan Labarai Da Hulda Da Jama'a Na Hukumar INEC
Ministan harkokin wajen China Wang Yi da ya kawo ziyara Najeriya, yayi alkawarin kasarsa za ta ci gaba da tallafawa Afirka bayan ganawarsu da Shugaba Buhari.
Poland: Ayarin sojojin Amurka a Poland ya iso bakin iyaka da Germany a wani yunkurin karfafa NATO, yunkurin da Rasha ta kushewa.
Emmanuel Ogebe yayi magana akan muhimmancin sabuwar Dokar da 'yan majalisar Amurka suka kafa, dangane da Boko Haram.
Donald Trump Yayi Watsi Da Batun Cewa Rasha Tana Da Bayanan Sirrin Da Zasu Kunyata Shi
Shugaba Yahya Jammeh Na Gambiya Ya Ja Kunnen Kasashe Masu Neman Shiga Rikicin Kasarsa
Akalla mutum 50 suka mutu bayan wasu tagwayen bama-bamai da suka tashi a kusa da wani yanki da ke dauke da wasu ofisoshin gwamnati a Kabul.
Gambia: Shugabannin kasashen yammacin Afrika sun tafi Gambia domin matsantawa shugaba Yahya Jammeh ya amince da shan kaye a zaben da aka yi ya kuma sauka daga mulki.
Tashar talabijin din Iran ta bayar da sanarwar mutuwar tsohon shugaban kasar, wanda kuma ke kan gaba wajen kawo sauyi a kasar, Akbar Hashemi Rafsanjani.
Nigeria: Masu fafutukar ganin an dawo da ‘yan matan Chibok sun yi gangami a Abuja don nuna rashin amincewarsu da gazawar da gwamnati ta yi wajen kwato ‘yan matan da aka sace shekaru 2 da suka wuce.
Hira Tare Da Malam Chom Bagu Mai Bada Shawara Na Kungiyar SFCG, Disamba 13, 2016
Domin Kari