Babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Laftanal janal Tukur Buratai, ya yayi maraba da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu, Laftanar Janar Lindle Nyam, yayin da ya kai wata ziyarar aiki Najeriya.
A cewar jamar Turkur Buratai, sojojin Najeriya sun taka rawa sosai a atisayen da rundunar sojan Afirka ta Kudu ta shirya, da ma wasu da cibiyoyin ‘kasa da ‘kasa suka shirya a can baya.
Haka kuma sojojin Najeriya zasu ci gaba da taka rawa wajen ire-iren wadannan atisaye domin su fahimci kansu sosai, da zummar shawo kan matsalar tsaro dake addabar nahiyar Afirka.
Janar Turkur Buratai ya kuma tabo batun hadin kai wajen aiki tare kan musayar bayanan sirri, wanda ya ce zai taimakawa rundunonin sojojin biyu.
Taron kwamitin tsaro na Najeriya da Afirka ta Kudu da za a fara cikin wannan mako, wani ‘karin tabbaci ne da irin alakar tsaro dake tsakanin ‘kasashen biyu, inji Buratai.
A nashi bangaren babban hafsan sojojin Afirka ta Kudu, Janar Lindle Nyam, yayi tilawar irin dasawar sojan dake tsakanin Najeriya da kasar sa ne, yana mai cewa kasar sa ta amfana da irin tallafin da Najeriya ke yiwa kasarsa, musamman ta hannun kungiyar hadin kan Afirka ta OAU.
A cewar masanin tsaro mallam Kabiru Adamu, na ganin cewa a halin yanzu babu wata ‘kasa a nahiyar Afirka da rundunar sojojinta ta kai ta Afirka ta Kudu, ganin irin makaman da suka da su da kuma kimiyya da fasahar kirkiro makamai. Kuma kulla dangantaka tsakanin kasashen biyu zai iya taimakawa kamfanonin da Najeriya take da su, wajen bunkasasu su rika kirkiro makamai a cikin gida.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum