Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zauren VOA: Tattaunawa Kan Kalubalen Tsaro a Arewacin Najeriya


Iyaye mata, shugabannin al’umma da na kungiyoyi na daga cikin wadanda suka halarci wani zauren tattaunawa da Muryar Amurka ta shirya a ofishinta da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, a ci gaba da lalubo mafita dangane da matsalar tsaro da al’ummar kasar ke fustakanta.

Duk da ikirarin kokarin da gwamnatoci a Arewacin Najeriya ke cewa su na yi don kawo karshen matsalar tsaro da ake fuskanta a yankin, ciki har da garkuwa da mutane, yaduwar makamai a hannun daidaiku, da yadda ake samar wa 'yan ta'adda bayanan sirri, da kuma yadda ake halin ko in kula da matsala tun ta na karama da dai sauransu, su aka fi mai da hankali akai a taron na wannan karon.

Aliyu Shamaki, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya bayyana cewa rashin ilimi da cin hanci da rashawa na taka rawa a batun rashin tsaro a arewacin Najeriya, ya na mai cewa idan babu ilimi a arewacin Najeriya to an samu barakar farko akan batun kalubalen tsaro a yankin.

A nata bangaren 'yar’gwagwarmaya da ake kira da Mama Balaraba, ta yi kira ga sauran mata a yankin arewa da su fito don neman mafita ga sha’anin na tsaro.

Shi kuma Kwamred Aliyu Aminu waziri, mai magana da yawun kungiyar da ke kokarin tattauna yadda za a samu zaman lafiya a Najeria, ya ce kalubalen tsaro ba na gwamnati ne kadai ba dole sai al'umma ta sa hannu, a saboda haka yanzu suka fito da wani tsari na bin mutanen da aka saba musu kuma suka dauki makamai, za su tattaunawa da su don a samar da dorarren zaman lafiya.

Bayan nazari kan matsaloli na tsaro da yankin arewacin Najeriya ke fama da shi ya sa shugabannin sashen hausa na Muryar Amurka da su ka jagoranci taron wato, Grace Alheri Abdu, Hajiya Madina Dauda da Nasiru Adamu Elhikaya fitar da matsaya kan cewa tsaro shi ne kashin bayan bunkasar tattalin arziki wanda a kullum ake kuka da tabarbarewarsa, musamman a yankunan Arewacin Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00
Zauren VOA daga jihar Kaduna Alan Almajiranci da Cin Zarafin Mata - 3-1
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:55 0:00


XS
SM
MD
LG