Majalisar dokokin jihar Bauchi ta soma nazari akan wani kuduruin doka da zai samar da hukunci mai tsanani akan wadanda aka kama da laifin fyade da kuma cin zarafin mata.
Majalisar ta bayyana cewa tana da hakki a kan ta na ganin ta kirkiro dokar da za ta bada kariya da kuma dakile munanan ayyukan ta’addanci da wasu miyagun mutane da ke cikin al’umma ke aikatawa.
Kakakin majalisar, Abubakar Y. Suleiman, ya ce "a kan wannan batu, 'yan uwana 'yan majalisa sun ba da goyon baya dari bisa dari, a cikin muhawarar da muka yi ma akwai wadanda suka bada shawarar cewa a fara yanke hukuncin kisa kan masu aikata fyade."
Rahottani daga jihar na bayanin cewa a kullum akan sami rahoton cin zarafin mata da su ka hada da fyade da kuma dukan mata a sassa daban na jihar, kamar yadda shugaban kungiyar Ash Foundation da ke kare hakkokin mata, Comfort Attah ta shaida wa Muryar Amurka.
Bincike na nuni da cewar yawancin wadanda ake aikata fyaden a kan su masu karancin shekaru ne da ake yaudararsu ta hanyoyi daban-daban.
A cikin kwannakin nan ana ci gaba da samun karuwar lamuran fyade a duk fadin Najeriya.
A safiyar yau Litinin ma, Sufeto Janar na ‘yan sanda Mohammed Adamu ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari bayani akan matsalolin fyade a kasar.
Facebook Forum