Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAUREN MATASA: Yadda Damina Ta Kankama Amma 'Yan Bindiga Su Ka Hana Shiga Gonaki Da Ke Nesa Da Gari, Kashi Na 4 - Agusta 28, 2023


Nasiru Adamu
Nasiru Adamu

Ci gaba da Zauren Matasa a garin Dan Umaru mai albarkar matasa manoma da ke karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi ta arewa maso yammacin Najeriya.

Matasa sun taru a zauren inda su ka koka da cewa ga dai damuna ta kankama amma miyagun iri sun hana shiga gonaki da ke nesa da gari.

Matasan na bukatar dauki daga hukumomi don kar hakan ya zama barazana ga samar da abinci yayin da janye tallafin fetur ya jefa talakawa cikin kuncin rayuwa.

Ra'ayin matasa na nuna ko dai ba za a samu yin noman yanda a ka saba ba; to mutane su samu yin barci da ido biyu rufe.

A makon jiya Muhammad Bara'u ya ce matsalar a baya sai dai a majigi su ke gani amma yanzu ga ta nan a zahiri.

Saurari shirin:

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG