Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Mr Yakubu Dogara, ya gabatar da takardan koke gaban Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda kasar, wadda a ciki ya ke zargin cewa wasu daga cikin jami'an 'yan sandan sun hada baki da wasu mutane masu shirin kashe shi.
Takardan koken mai dauke da rattaba hannun tsohon Kakakin, wadda aka raba wa manema labarai nan Bauchi, ta yi zargin cewa wasu 'yan sanda da tsohon Kakakin Majalisar ya bayyana da sunan da Sufeto Dakat Samuel, da Sufeto Auwalu Mohammed, sun hada baki da wani mai suna Barau Joel Amos, mai lakabin Sarkin Yaki, wajen Kulla makircin neman raba shi da ransa.
Cikin wasikar da ya rubuta, tsohon kakaki Dogara, ya ce, ya tabbata cewa Sufeto-Janar Na 'Yansandan Najeriya, Usman Baba Alkali, na sane da wannan lamari tun da al’amari ne da ya shafi sata a runbun adana makaman ‘yan sanda da ke Bauchi, wanda jami’an da aka ba su amanar tsare su su ka yi, inda Barau Joel Amos, ya nemi sayen su, ko kuma ya kasance yana sayen bindigogi daga jami'an.
Mr Yakubu Dogara ya ce“An sanar da shi cewa Barau Joel Amos ya amsa cewa dalilin da ya sa ya nemi sayen bindigogin shi ne ya kashe shi da wasu mutane uku daga cikin mazaban sa, ciki har da Barista Istifanus Bala Gambar, Rev Markus Musa (Shugaban CAN, T/Balewa). ) da Emmanuel (Shugaban NL, T/Balewa)
Sai dai a na ta ba’asin, rundunar 'yan sandan Jihar Bauchi, ta bakin kwamishinan 'yan sandan Jihar, Umar Mamman Sanda, ta ce batun ba haka ba ne, amma ta na bincike akai kuma ta kama wani da ya amsa cewa ya yi niyyar sayen makamai don kashe Dogara da wasu mutane.
Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad: