A cewar wani mai suna Daniel Daniel, abu mai muhimmanci a ziyarar da shugaba Buhari ke yi a wadannan jihohi shine zantawa da matasa ‘yan kabilar Igbo, domin jin dalilin da yasa suke neman ballewa daga Najeriya, dan kafa kasar Biafra.
Da dama daga cikin wadanda suka bayyana ra’ayoyi su dangane da ziyarar shugaban kasa a wannan yanki, sun nuna bukatar zantawa da shugabanni da matasan yankin domin tabbatar da fahimtar irin yanayin da jama’ar yankin ke ciki.
A cewar wani dan arewa mai zama a kudsancin Najeriyar, wasu daga cikin ‘yan kabilar Igbo, sun bayyana farin cikin su ganin yadda gwamnatin tarayya ta kudiri aniyar gyaran babbar hanyar data shiga birnin Onicha.
Alhaji Musa Sa’idu, shine shugaban ‘yan arewa mazauna kudancin Najeriya, ya bayyana cewa farin cikin da shugabannin ‘yan kabilar Igbo suka nuna a sakamakon ziyarar, na nuni da irin hadin kai da kuma dankon zumunci tsakanin gwamnati da ‘yan kabilar.
Wannan ziyara ita ce ta farko da shugaba Mohammadu Buhari ya kai a yankin mai kokarin ballwa daga Najeriya tun bayan hawansa karagar mulki, duk da barazanar da kungiyar fafutukar ballewa daga kasar ta yin a barazanar tada tarzoma a lokacin ziyarar.
Daga Fatakwal, ga rahoton da Lamido Abubakar ya aiko mana.
Facebook Forum