Shugaban kamfanin “Niger Links” dake hulda da kamfanomnin ketare masu zuba jari a Najeriya, Thessa Bagu, ta bayana haka da nuna cewa kamfanonin zasu shiga Najeriya a cikin wannan makon domin ganawa da masu cinikayya da kuma raba hajar lantarki.
Kamfanonin dake wakiltar wasu masana’antun lantarki 7500, na kasar Turkiyya, zasu zo da hajjar wayoyin wutar kayan Lantarki da suka shafi na rarraba wutar bugu da kari Tac tace kamfaninin sukan fitar da kayan lantarki a kasuwar duniya duk shekara da suka kai dalar Amurka biliyon 10.
A irin wannan zuba jari Gwamantin Najeriya, na bayyana fita daga fatara ta kuma yadda tattalin arziki Najeriya ke kara samun ta gomashi.
Duk da yake akwai tasiri, farfadowar tattalin arzikin na tafiyar hawainiya domin talakawa dake shan dakar kuncin, amma abubuwa sun inganta idan an kwatanta da bara daidai wannan lokaci kuma akwai kyakkyawan fata ga Najeriya inji Ministan kudin Najeriya Kemi Adeoshun.
A baya shugaba Buhari ya ziyarci kasar Turkiyya inda ya halartar taron kungiyar kasashe 8, da kuma kira ga Turkiyya da ta dakile sumogal din makamai zuwa Najeriya, a baya an kama makamai da dama da akayi odarsu daga Turkiyya zuwa Najeriya, da ake zargin masu son tada fitina suka yi oda.
Facebook Forum