Jarumi Adam A. Zango ya sauya dan takarar shugaban kasar da yake marawa baya a babban zaben da za a yi a Najeriya nan da wasu kwanaki masu zuwa.
Dan wasan kwaikwayon ya shiga shafinsa na Instagram a yau Laraba, ya wallafa wani hoto, wanda ya nuna shi ya daga hannun Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkarshin jam’iyyar PDP, alama da ke nuna cewa ya koma goyon bayansa.
“An ba ni mukamin jakadan jam’iyyar PDP.” Zango ya rubuta a shafin nasa na Instagram.
A da, jaurmin na dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood wanda har ila yau mawaki ne, yana goyon bayan shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda yake takara karkashin jami’yya mai mulki ta APC.
A karshen shekarar da ta gabata, har ma uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, ta karrama shi da lambar yabo , yayin da aka fara yakin neman zabe.
Atiku shi ne babban abokin hamayyar shugaba Buhari a zaben wanda za a yi a ranar 16 ga watan nan na Fabrairu.
A kwanakin baya, Zango, wanda ake wa lakabi da “Prince Zango” ya halarci tarukan yakin neman zabe na APC inda ya yi wakoki da kira da a zabi shugaba Buhari da jam’iyyarsa ta APC.
Martani
Jarumi Adam A. Zango bai bayyana dalilinsa na sauya sheka ba, amma masu lura da al’amuran yau da kullum da ke faruwa a dandalin na Kannywood da wasu abokanan sana’arsa, sun yi ta tsokaci kan wannan mataki da ya dauka.
Sarkin wakan San Kano, Nazir Ahmad, na daya daga cikin fitattun masu nishadantarwa da suka fara mayar da martini kan sauya shekar da Zango ya yi.
“Ka kira mutane kar su sayar da kuri’arsu, kar su sayar da ‘yancinsu, ka ce ko za a kashe ka sai Buhari….saboda ba a baka kudi ba kawai shi kenan sai lissafinka ya karye sai ka tafi.” Inji Sarkin Nazir Ahmad kamar yadda ya wallafa a wani bidiyo a shafinsa na Instagram.
Ya kara da cewa, “Ku kuna cewa mutane su yi don Allah, ku kuma kuna yi don kudi.”
Sai dai Chizo_1_germany_k, wani fitaccen mai wallafa hotuna da bidiyon barkwanci a shafin Instagram mazaunanin kasar Jamus wanda shi ma a da jarumi ne a Kannywood, ya ce yana ganin, zaluntar Zango aka yi, shi ya sa ya koma PDP.
“Wannan tafiyar da Zango ya canza, wallahi! Wallahi!! yana daya daga cikin zaluncin da ake yi a Kannywood. An san cewa Adam A. Zango masoyin Baba Buhari ne amma sanadiyar kuntata mai da ake yi, ga shi yanzu mun yi losing dinsa (rashin shi), ya bar tafiyar Baba Buhari ya koma tafiyar Baba Atiku.” Inji Chizo_1_germany_k
“Adam A. Zango, Allah ya taimake ka.” Chizo_1_germany_k, Chizo ya kara da cewa.
Ita kuwa Hauwa Waraka, fitacciyar jaruma, cewa ta yi “Mu dai zama daram a APC.
Wani fitacce jarumi da shi ma ya garzaya shafinsa na Instagram ya yi magana shi ne Abba Al Mustapha., amm shi lale marhabin ya yi da matakin da Zango dauka.
"Barka da zuwa dan uwa." Inji Abba wanda ya wallafa hotonsa da Zango suna gaisawa.
Sashen Hausa na Muryar Amurka, ya yi kokarin tsakuro kadan daga cikin irin tsokacin da mabiya shafin Instagram din Zango suka yi, amma ga dukkan alamu ya kulle sashen yin tsokaci.
Yanzu Adam A. Zango, ya hada sheka da jarumai irinsu Sani Danja, Fati Muhammed, Al Amin Buhari, Zaharaddeen, da Teema Makamashi a yi wa Atiku yakin neman zabe.
A gefe guda, Zango ya baro su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Rukayya Dawayya, Halima Atete, Jamila Na Gudu, Nuhu Abdullahi da Maryam Yahaya a jerin juaramn da ke goyon bayan shugaba Buhari.
Ba a dai taba wani lokaci da jaruman na Kannywood suka samu rarrabuwar kawuna ta fuskar siyasa ba, sai a wannan kakar zabe, kamar yadda masu lura da al’amuran Kannywood ke cewa.