Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsara Zanga-Zangar Da Ake Shirin Yi Ta Zamo Tamkar Ta Kenya - Hukumomin Soja


 Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron, Manjo Janar Edward Buba
Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron, Manjo Janar Edward Buba

A yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja a yau Alhamis, daraktan yada labaran ma’aikatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba yayi gargadin cewar sojoji ba zasu kyalle Najeriya ta fada cikin hayaniya ba.

Gabanin zanga-zangar gama-garin da ake shirin gudanarwa a fadin Najeriya akan matsin tattalin arziki, hukumomin soja sun ja kunnen masu shiryata dasu guji duk wani nau’i na tashin hankali.

Ya bayyana cewa manufar masu shirya zanga-zangar ita ce kwaikwayon boren daya faru a kasar Kenya dake shiyar gabashin Afirka wanda ya rikide zuwa tashin hankali.

A cewar Janar Buba, duk da cewa ‘yan kasa nada ‘yancin fitowa su bayyana korafe-korafensu, hukumomin soji ba zasu amince da kowane irin gangamin tashin hankali ba.

Ya kara da cewa hukumomin sojan sun bankado shirin da wadansu batagari ke yi na sauya akalar zanga-zangar zuwa ta tashin hankali ta hanyar afkawa ‘yan Najeriyar da basu ji ba basu gani ba tare da harkokin kasuwancinsu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG