Wata sanarwa mai dauke da sa hanun mai bashi shawara kan yada labarai da hulda da jama’a, Femi Adesina, ta ce Buhari ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da shugaban Ghana John Dramani Mahama, a wata ziyarar aiki ta yini guda da ya kai Ghana.
“Bayan ranar 30 ga watan Satumba, ku tuhume ni idan ban nada ministoci na ba.” In ji Buhari, yayin da ya ke amsa tambaya kan dalilin da yasa bai nada ministocinsa ba.
Buhari har ila yau ya ce gwamnatinsa na yin galaba a kan ‘yan kungiyar Boko Haram tun bayan da ya kama mulki tare da taimakon dakarun hadin gwiwa na kasashen waje.
“Abin da na yi na farko shine a sake kintsa dakarun Najeriya tare da basu umurni mara sarkakiya, kamar a fannin abinda ya shafi horaswa da samar musu da kayan aiki da kuma yadda aka rarraba su.” Buhari ya ce.
Ya kuma ce a arewa maso gabashin kasar, ana samun canji domin an rutsa ‘yan kungiyar ta Boko Haram a dajin Sambisa.
“Sannan a hankali ‘yan gudun hijra na komawa muhallansu, yayin da muke kokarin mu ga cewa sun koma rayuwarsu kamar ta da.”
Da farko, shugaban Ghana, Mahama ya ce sun tattauna da takwaransa na Najeriya inda suka cimmam matsayi kan batutuwan da suka shafi huldar kasuwanci da samar da tsaro a yankunansu.