Wani mai magana da yawun Fadar White House ya ce ya rage ma gwamnatin Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ta zabi amincewa da bangaren leken asirin kasa na Amurka ko kuma kasar Rasha da Wikileaks.
Josh Earnest na amsa tambaya ne kan zargin da Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi cewa, gwamnatin Shugaba Barack Obama na yin makarkashiya ga Trump ta wajen yada labaran karya.
Putin ya ce yada wani labarin abin fallasa, wanda ba a san tushensa ba da aka yi makon jiya, wanda ke kunshe da zarge-zargen tabargaza game da Trump, wani bangare ne na yinkurin abin da ya kira, "yin zagon kasa ga halalcin Shugaba mai jiran gadon" duk kuwa da cin zaben Shugaban kasa kiri-kiri da Trump ya yi.
Putin ya bayyana wani zargin da aka yi a cikin kundin tabargazar cewa Trump ya yi ta lalata da karuwai a wani otal na birnin Mascow a 2013 da cewa zargin "kazafi ne kawai." Putin ya kara da cewa wadanda su ka tsara kazafin "sun ma fi karuwai lalacewa," sannan ya jefa ayar tambaya kan yadda za a yi ma Trump, a ta bakinsa, "ya bukaci karuwai, bayan kuwa ya yi ta harka da mata mafiya kyau a duniya."