A jamhuriyar Nijer hukumar zaben kasar da hadin gwiwar kungiyar masu rajin kare Dimokradiya sun shirya wata mahawara da nufin ganar da matasan kasar amfanin kafafen sada zumunta a lokacin zabe.
La’akari da yadda masu yada labaran bogi ke cin karensu ba babbaka a kafafen sada zumunta, da nufin cimma wata mummunar manufa, wanda kuma hakan ke barazana ga zaman lafiya, ya sa kungiyar’yan rajin kare dimokradiya da ake kira CADENE shirya wannan mahawara domin wasu gomman matasa da zummar ganar da su hanyoyi mafi a’ala na amfani da irin wadannan kafafe a lokacin zabe. Ibrahim Awal Oumarou, mamba a wannan kungiya, ya jaddada muhimmancin daukar wannan mataki tun yanzu.
Kakakin hukumar zabe ta kasa ta CENI, Nafiou Wada ya ce hukumar ta yi na’am da wannan yunkuri na matasan CADENE domin abu ne da zai bada damar dakile hanyoyin yada jita jita ko kuma labaran bogi inji shi.
A ranar 13 ga watan disamban da ke tafe ne ake sa ran gudanar da zaben kananan hukumomi a nan Nijer, yayin da aka bayyana ranar 27 ga watan na Disamba a matsayin ta zaben ‘Yan Majalisar Dokokin Kasa hade da zagayen farko na zaben Shugaban Kasa saboda haka hukumar zabe ta dauki alkawarin wallafa bayanai akai akai game da sha’anin gudanar zabe I zuwa lokacin fitar da sakamako a shafinta na yanar gizo sabili kenan ta ke kiran jama’a akan bukatar takatsantsan da masu yada bayanan bogi a kafafen sada zumunta.
Ga cikakken rahoton Souley Barma a sauti:
Facebook Forum