Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN KASAR GHANA: Bawumia Yace Zai Soke Wasu Haraji Idan An Zabe Shi Shugaban Kasa


Bawumia
Bawumia

Mataimakin Shugaban kasar Ghana, Dokta Mahamudu Bawumia, ya yi alkawarin zai kawar da wasu nau’oin haraji da gwamnati mai ci ta aiwatar, musamman harajin hada-hadar kudi na lantarki (E-Levy), idan aka zabe shi Shugaban kasa a babban zaben kasa mai zuwa.

Yayin da yake gabatar da jawabinsa ga al’ummar kasa na farko, bayan an zabe shi a matsayin dan takaran shugaban kasa, a karkashin jam’iya mai ci ta NPP, Mataimakin Shugaban kasa, Dokta Mahamudu Bawumia, ya bayyana manufofin da yake da aniyar cikawa idan an zabe shi yana mai cewa,

"A matsayina na mataimakin Shugaban kasa, ni tamkar kwandestan direba ne, amma da yardar Allah, idan ku ka mai da ni Shugaban kasa, zan kasance a kujerar direba tare da ikon da tsarin mulki ya ba ni ."

Taron jami'yya a Ghana
Taron jami'yya a Ghana

Dokta Bawumia ya bayyana gudunmawar shawarwarin da ya bayar ga kwamitin tattalin arzikin kasa, wanda yace, an samu ci gaba a tattalin arziki a baya-bayannan, kuma ya bayyana aniyarsa na rage nauyin dake kan gwamnati ta hanyar amfani da kamfanoni masu zaman kan su wajen karfafa tattalin arziki idan an zabe shi.

Haka kuma ya bayyana karara cewa, zai soke harajin hada-hadar kudi na elektronika (e-levy) da wasu nau’oin haraji da wannan gwamnatin ta kirkiro domin hijira zuwa ga tattalin arziki na dijital.

Da yake tsokaci kan jawabin na mataikin Shugaban kasar, Seeba Shakibu, shi ne Sakataren Jam’iyar PNC na yankin Greater Accra, yace duk kaddamar da kudurorin wannan gwamnatin da shi ake yi.

Taro a Ghana
Taro a Ghana

"Duk abinda ya karanto, muna ganin kanzon kurege ne kawai, saboda ababan da yace zai soke idan ya hau kan karagar mulki, ai a gabansa aka tabbatar da su; da shawararsa Shugaban kasa Nana Akufo-Addo ya zartar da su."

Sakataren jam’iyar CPP na yankin Ashanti, Issah Abdul Salam a nasa bangaren yace jama’ar kasar Ghana ba su manta da alkawuran shi da jam’iyarsa suka yi wa kasa, kuma ba su cika ba.

Taron ya samu halartar jiga-jigan jam’iyar NPP mai ci, da suka hada da tsohon shugaban kasa, John Agyekum Kuffour, da matar Shugaban kasa, Rebecca Akufo-Addo, da Shugaban jam’iyar da sauransu.

Saurari rahoton Idris Abdullah:

Bawumia Yace Zai Soke Wasu Haraji Idan An Zabe Shi Shugaban Kasa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG