Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Amurka: Ba Rasha Ta Kar Zomon Ba - In ji Putin


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Kamar yadda ya yi a baya, Shugaban Rasha Vladimir Putin ya nesanta kasarsa da galabar da Shugaba Donald Trump ya yi kan tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton. Ya ce masu kokarin nuna rashin halalcin gwamnatin Trump ne su ka kago almarar cewa Rasha ce sanadi.

Jiya Alhamis Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi watsi da zargin cewa kasar Rasha ta yi katsalandan a zaben Shugaban Amurka na bara, sannan ya kara da cewa masu adawa da Shugaban Amurka Donald Trump ne su ke yada jita-jitar saboda kawai su nuna gwamnatinsa ba ta da halalci.

Da ya ke magana akan batutuwa masu dama yayin hira da ‘yan jarida da yak an yi shekara shekara a birnin Mascow, Putin ya yi fatan dangantakar Amurka da Rasha za ta ingantu kamar da.

Hukumomin leken asirin Amurka sun yi ittifaki kan cewa Putin ya bayar da umurnin daukar matakan da za su yi tasiri kan zaben Amurka ta yadda Trump zai yi galaba kan tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton. Tump dai ya ce kwamitin yakin neman zabensa bai hada baki da Rash aba.

Putin ya yi watsi da zargin yin katsalandan din da cewa kage ne kawai sannan ya ce masu wannan zargin na yin illa ne kawai ga Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG