Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: An Yi Kira Ga IGP Da Ya Kama Dan Takarar Gwamna Na Jami'iyar YPP A Jihar Akwa Ibom


IGP Alkali Baba Usman
IGP Alkali Baba Usman

Gamayyar kungiyar masu fafutukar tabbatar da gaskiya da shugabanci nagari a Akwa Ibom sun yi kira ga babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba da ya kama Sanata Bassey Albert Akpan, dan takarar gwamna na jam’iyyar Young Progressives Party, YPP, kuma Sanata mai wakiltar mazabar Uyo.

Kungiyoyin sun bukaci da a yi masa tambayoyi bisa zargin tunzura jama'a da yin barazana ga rayuwar wasu fitattun 'yan asalin karamar hukumar Ibiono Ibom ta jihar.

Koken dai yana mayar da martani ne ga wani faifan bidiyo da ake yadawa, inda aka ga Sanata Akpan, yana rera take, yana mai cewa “Zan yake su! Dokta Iniobong Essien, Mista Aniefiok Iwaudofia, Ini Ememobong, Ime Okon wanda shi ne zababben dan majalisar wakilai, da Godwin Ekpo wanda shi ne dan takarar jam’iyyar PDP a zaben kujerar majalisar wakilai a zabe mai zuwa. Ya ce yana gani ba cikakkun ‘yan asalin Ibiono Ibom ba ne."

Sanata Akpan dan asalin karamar hukumar yankin ne.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Dr. Akaninyene Utuk da Sakatare, Engr. Godswill Akpan kuma suka bayyanawa manema labarai a Uyo a ranar Juma’a, gamayyar kungiyar ta bukaci hukumomin tsaro da na kasa da kasa da su dora alhakin kashe duk wani dan asalin yankin a kan Sanata Bassey Albert idan hakan ya faru ko kuma aka samu barkewar rikici a zaben gwamnan da za a yi yau Asabar a yankin.

A yayin da ta ke amfani da kafafen yada labarai da dama don jawo hankalin hukumomin tsaro kan kalaman tunzura jama’a da ke kunshe cikin wani faifan bidiyo na yakin neman zabensa a karamar hukumar Ibiono Ibom, kungiyar ta bayyana mamakin yadda wani fitaccen dan yankin Ibiono Ibom kamar Mista Bassey Albert zai tunzura jama'a su tashi su raunata wasu kuma su raunata ’yan asalin kasar da ba su zabe shi da jam’iyyarsa ba.

Hakazalika, lauyoyin Dokta Iniobong Essien, Barista Ime Okon, Mr, Aniefiok Iwaudofia, Godwin Ekpo, da kuma Kwamared Ini Ememobong sun roki babban sufeton ‘yan sandan kasar da ya gaggauta gayyato Mista Albert domin amsa tambayoyi kan abin da suka kira matakin da Mista Albert ya dauka na yin kalaman tsano da kiyayya ga mutanen da suke kare su.

A cikin wata wasikar koken da muka samu, masu shigar da karar sun kawo misali da sashe na 45 na kundin laifuffuka na jihar Akwa Ibom da ya haramta yada yakin wariya na zama dan asali da kuma tanadin hukuncin hukunta masu laifi.

Masu gabatar da kara a cikin bukatunsu sun bukaci ‘yan sanda da su gaggauta gudanar da bincike kan zargin da kuma gurfanar da wanda ya aikata laifi gaban hukuma.

XS
SM
MD
LG