A cewar mai martaba sarkin Kwandare da aka mikawa sandar girma zuwa sarki mai daraja ta daya Alhaji Ahmadu aL-Makura, jama'a su tabbatar sun karbi katin zabe na din-din-din su kuma yi zabe isa ga cancanta,
Sarki Ahmadu yace su suna rokon duk 'yan Najeriya da suka cika shekaru 18 zuwa sama su karbi katinsu, wato kowa ya tabbatar makaminsa na hannusa.Yace kowane sarki a jihar bai huta ba domin yana son a yi zabe lafiya. Idan aka fito daga sallar Juma'a suna kiran jama'a su jajarce su tsaya a yi zabe lami lafiya. Yace abubuwan da suka faru a shekarar 2011 bayan zabe basu ji dadinshi ba su sarakuna.
Yanzu matasa sun tabbatar masu cewa a wannan karon ba zasu yadda a yi anfani dasu ba a tada hargitsi.
Saidai har yanzu wasu na korafin rashin samun katin zaben. Wasu sun ce sun sha yin zirga zirga zuwa inda suka yi rajista domin karban katinsu amma basu samu ba. Walau ko kada ma'aikatan su kasance a wurin bada katin ko kuma a ce masu babu hanyar yanar gizo.
Abubakar Aliyu Muhammad jami'in INEC mai hulda da jama'a ajihar Nasarawa yace daga katin zabe miliyan daya da dubu dari biyu sun zaba sama da dubu dari tara. Yace zasu cigaba da rabawa har su kammala.
Ga rahoton Zainab Babaji.