Bishop Idowu Fearon Anglican Archbishop jihar Kaduna yana cikin wadanda suka jawo hankali matasa a wurin wani taro da kungiyar matasa ta arewacin Najeriya wadda ake kira ACAC ta kira a Kaduna domin hada mabiya addinan biyu a zaben dake tafe.
Archbishop Fearon yace yakamata su gaya ma magoya bayansu cewa arewa fa mutanen arewa daya suke. Kada a yadda addinai biyun da Allah ya bayar su kawo rabuwar kawuna. Kur'ani da Bible duk sun fada Allah daya ne. Najeriya bata bukatan shugaba bisa ga addini amma tana bukatab shugaba musulmi ko kirista mai adalci wanda zai zama shugab ba wai domin addininsa ba. Ba addinin dan takara ake bukata ba amma bin addininsa ake bukata.
Shi ma Sheikh Ahmed Abubakar Gumi yana cikin malaman da suka fadakar a taron. Yace idan ana son a cimma nasara ya zama wajibi a yi hakuri. Yace matasa su ne wuka su ne nama a wurin zaman lafiya saboda haka tunda su ne suka dauki yunkurin za'a ga banbanci.Duk abun da aka saka tsanani a ciki sai ya lalace. Kuma duk abun da aka yi da sauki sai ya gyaru. Dole idan ana son a ci nasara dole a yi hakuri da yin abubuwa da lallama. Domin sun rabu bisa ga siyasa kada su yi fada. Amma yace yana son su san cewa rikicin da ake yi da duniya ne kada su saka addini ko kabilanci ciki.
Alhaji Aminu Daram daya daga cikin daraktocin kungiyar yace sun shirya taron ne domin mutane su koma karkara su kafa kwamiti na akalla mutane ashirin da biyar biyar a kowace hukuma domin su dinga wayarwa matasa kawuna akan horaswar zaman lafiya da suka samu. An yi horaswan ne akan yadda za'a kwantar da hankalin mutane idan takaddama ta taso kuma a rage kiyayya dake tsakanin musulmai da kiristoci. Kada kuma matasa su bari wasu 'yan siyasa su yi anfani dasu wajen kone-kone da kashe-kashe.