Masu zanga zanga anan birnin Washington, sunyi maci da kin cin abinci na sa'o'i 24, a harabar fadar white ta shugaban Amurka, domin nuna bacin ransu kan abunda suke gani na rashin daukan mataki da Amurka take yi, kan kisan kare dangi da ake yi a yankin Darfur na Sudan.
Zanga zangar bangare ne na wani shiri a "duk fadin duniya" na daukan matakai na yin Allah wadai kan kisan kare dangi a Darfur, gwagwamaryar da ake ci gaba da yi har zuwa ranar Litinin, 25 ga watan nan.
Kimanin masu zanga zanga dari ne suke cewa "A hana kisan kiyashi a Darfur," da kuma "adalci- adalci a Darfur," a harabar fadar shugaban na Amurka.
Ni'emat Ahmadi, wacce ta kirkiro kuma shugabar kungiyar mata masu fafutukar ganin an dauki mataki kan rikicin na Darfur, ta gayawa, Shirin Muriyar Amurka da ake kira South Sudan in Focus" da turanci cewa, ta shirya zanga zangar harda kin cin abinci, domin mutane suna mutuwa, kuma fadar White Hoiuse bata yin wani abu akai.
"Muna neman ganin gwamnatin Obama ta fara sukar abunda yake faruwa, kuma ta tura sojoji na musamman zuwa Darfur, domin su taimakawa al'amarin. Mutane suna ta mutuwa domin matakan da gwamnatin Sudan take dauka, shi yasa muke son shugabannin duniya, musaman gwamnatin Amurka, ta tsawata kan hare haren da ake kaiwa a yankin Darfur, kuma alhakin haka, yana kan gwamnatin kasar Sudan.
An zafafa fadan da ake yi tsakanin gwamnatin Sudan, da 'yan tawaye a yankin Darfur a a baya bayan nan. Rikicin ya samo asali tun shekara ta 2003.