Hukumar alhazan Nigeria ta ce ranar 21 ga wannan watan na Yuli ne zata fara jigilar alhazai zuwa kasa mai tsarki. A wannan shekara za’a fara ne da alhazan jihar Kogi wadanda zasu tashi daga Abuja.
A wani taron masu ruwa da tsaki da shugaban hukumar alhazan Barrister Abdullahi Mukhtar ya jagoranta an yi la’akari da wasu sabbin tsare tsare.
Gwamnatin Saudiya ce ta fito da sabbin tsare tsaren. Sabon tsarin yana tanadi cewa wajibi ne a san wadanda zasu yi aikin hajji kafin karshen watan Rajab alhali kuwa a Nigeria ba’a maganar zuwa hajji sai bayan watan Ramadan. Amma yanzu gwamnatin Saudiya ta ba da dama har zuwa karshen watan Shawal.
Abinda yafi daukan hankali a wajen taron shi ne batun adashin gata da shi Abdullahi Mukhtar ya bayyana yadda za’a yi. Sauye sauyen da Saudiya ta kawo ya sa hukumar alhazai ta kasa ta umurci jihohi su soma karban kudin ajiya daga wadanda suke son yin aikin hajji nan da shekara biyar. Mutane na iya biyan kudinsu kadan da kadan.
Gwamnatin tarayya na nazarin dokokin da zata kafa domin tabbatar cewa alhazan da zasu yi ajiya babu wanda ya cinye masu kudinsu. Haka kuma za’a tabbatar an saka kudinsu cikin kasuwanci na halal domin samun ribar da za’a ba alhajin. Itama Gwamnati zata samu nata rabon. Idan kudin Alhaji ya isa kudin kujerar hajji ba sai ya kara wani kudi ba domin za’a yi amfani da ribarsa a cika masa kudin zuwa hajji.
Yanzu kuma tun daga gida Nigeria za’a dinga daukan hoton yatsun alhazan.
Shugaban kungiyar shugabanin hukumomin alhazai na jihohi, Abubakar Sarkin Pawa Danko ya ce, jihar Zamfara tuni suka shirya tsaf. A kasa mai tsarki sun tanadar da masauki da masu ciyar dasu da motocin sufuri da dai sauransu.
A saurari rahoton Medina Dauda
Facebook Forum