Bayan nazari da mahawara akan makaloli 19 da shehunan malamai daga Jami’o’i da cibiyoyin binciken harkokin ilimi na ciki da wajen Najeriya, mahalarta taron sun gabatar da kudurori da dama wadanda ke kunshe cikin takardar bayan taro da aka fitar a zauren taro na tsangayar nazarin aikin lauya ta Jami’ar Bayero, Kano.
Dr Kabiru Haruna Isa, yace shawara ta farko ita ce a ci gaba da yin irin taron domin masana su zo su tattauna su yi nazari akan matsalolin al’umma su kawo ainihin mafita.
An kuma bada shawarar cewa harkar ilimin mata a bashi mahimmanci da abubuwan da suka shafi harkokin iyali da matsalolin damunsu. Ya kamata a kallesu da idon basira
Sannan an bada shawarwari akan matsalolin bara a cikin al’umma da kuma matsalolin dangantaka tsakanin addinai
Wani mutum mai sunaAliyu Muhammad ya ce taron ya zaburar dasu akan abubuwan da suka shafi addini da siyasa. Shi ma Ahmad Rashid Makarfi y ace ya koyi mahimmancin zaman lafiya akan cewa duk wani shugaba wajibi ne ya hada kan jama’arsa ya tabbtar da zaman lafiya
Dr Umaimah Al-Turabi na daga cikin ‘yayan magayi Sheikh Hassan Al-Turabi ya Haifa, wadda ta baiyana farin ciki da taron da aka yi akan ayyukan mahaifnta
A karshen dai wadanda suka shirya wannan taro sun sha alwashin mika abubuwan da aka cimma ga hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki domin dubawa.
A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani
Facebook Forum