Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya jaddada cewar za’a gudanar da zabe a ran Talata mai zuwa, zaben da shine na karshe a zagayen zabukan da ake yi a Nigeria cikin shekarar 2011.A jawabin day a yiwa al’ummar Nigeria ta kafofin sadarwa ran Alhamis, shugaba Goodluck Jonathan yace an dauki matakan tsaro yadda ya dace, kuma al’amura sun fara daidaituwa, bayan rikicin da ya biyo bayan sakamakonzaben shugaban kasa don haka babu wani dalilin da zai hana gudanar da zabe na gaba, wato zaben Gwamnonin jihohi da ‘yan majalisar wakilai. Kungiyar agaji ta Red Cross ta bada rahoton cewar rikicin siyasar da ya biyo bayan sakamakon zaben shugaban Nigeria ya janyo jikkatar mutane 410, sannan mutane sama da 40,000 ne suka rasa muhallinsu.
Za’a ci gaba da gudanar da sauran zabukan da suka rage a Nigeria duk da Tashin rikice-rikicen siyasa
Kwararrun masana da fashin bakin harkokin siyasar Nigeria sun yi hangen cewa, zaben Talata mai zuwa zai fi kowane hatsarin haduwa da rikicin siyasa. Amma shugaba Goodluck Jonathan yace za’a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024