Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Goodluck Jonathan ta karyata cewa ta tafka magudi a zaben shugaban kasa da aka yi ranar Asabar da ta gabata.
Da yake magana da wakilan kafofin yada labarai na cikin gida da ketare a Abuja,Ministan yada labarai Labaran Maku,yace PDP bata yi magudi ba.Yace idan da PDP tayi magudi da CPC jaririyar jam’iyya, da bata da karbuwa ko madafu, ba zata sami nasara a jihohin da suke hanun PDP ba.
Amma da suke mai da martani,dan takarar gwamna a tutar CPC a jihar Bauchi Architect Mohammed Dewu,yace PDP tana kokarin haddasa a husuma cikin jam’iyyar a zabe mai zuwa.Haka shima wani sabon dan majalisar tarayya a inuwar CPC daga mazabar Dukku yayi zargin PDp tana amfani da madafun iko wajen samun nasara.
Amma da yake magana,babban mukaddashin sakatare na PDP na kasa,Dr. Musa Babayo,yace PDP tana da matsaloli da suka ishe tab a bata da lokacin shiga sharru ba shanu d a ake zarginta dasu.